Murnar Atiku, Kwankwaso, Saraki za ta koma ciki, PDP ba ta kai takarar 2023 zuwa Arewa ba
- Ana rade-radin PDP za ta ba mutumin Arewa dama ya rike mata tuta a zaben 2023
- Mark Jacob yace jam’iyyar adawar ba ta tsaida magana kan wanda za a ba tikiti ba
- Tsohon Mai ba PDP shawara kan harkar shari’a yace za a dauki matakin da ya dace
Jam’iyyar hamayya ta PDP ta musanya rahotonnin da ke yawo cewa an fitar da matsaya a game da yankin da zai yi takarar shugaban kasa a 2023.
Mark Jacob ya ce ba a fara batun 2023 ba
A cewar jaridar The Nation, rahoton da ke nuna za a fito da wanda zai yi wa PDP takarar shugaban kasa daga Arewa a zabe mai zuwa, bai tabbata ba.
Wani tsohon mai bada shawara a kan harkokin shari’a a jam’iyyar PDP, Mark Jacob ya bayyana haka.
Mark Jacob ya taba rike kujerar kwamishinan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin jiha a Kaduna ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi.
Da aka zanta da shi a shirin safiya na “The Morning Show” a gidan talabijn Arise a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, Jacob ya musanya wannan.
“Babu wanda ya yi maganar inda za a kai mulki a jam’iyyarmu. Ba mu kai tikitin shugaban kasa zuwa Arewa ba.”
“Asali ma abin da wasu ‘ya ‘yan jam’iyya suke sha’awa shi ne a kai takarar zuwa bangaren kudancin kasar nan.”
Barista Mark Jacob shi ne ya fara musanya wannan batu, ya nuna shugabannin PDP za su dauki matakin da ya fi dace wa domin kai ga nasara a zaben 2023.
Jigon na PDP ya bayyana cewa duk da haka kowa yana da damar da zai furta ra’ayinsa a tsarin siyasa, amma ba za a dauki matakin da zai jawo bakin-jini ba.
Mun samu labari cewa da aka tambayi sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan kan batun yankin da zai samu tikiti, yace ba a dauki matsaya ba.
Za a ba Arewa dama a 2023?
A baya an ji kishin-kishin PDP na iya tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa, sannan wanda zai zama sabon shugaban jam’iyyar zai fito daga Kudu.
‘Yan siyasar da za su yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 suna kokarin cusa mutanensu a majalisar NWC domin su samu tikitin shiga takara cikin sauki.
Asali: Legit.ng