Ba zan cigaba da lamuntar ta'addanci ba, Lalong ga shugabannin Jos
- Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ja kunnen shugabannin karamar hukumar Jos ta arewa
- Ya ce su yi gaggawar kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a bangarensu don gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar hakan ba
- Gwamnan ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin da daddare yayin wani taro da suka yi a gidan gwamnati da ke Rayfield a Jos
Jos, Filato - Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ja kunnen shugabannin karamar hukumar Jos ta arewa a kan su yi gaggawar kawo karshen rikici da ta’addancin yankin.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin ta dare yayin wani taro a gidan gwamnati da ke Rayfield, Jos tare da masu ruwa da tsakin yankin a matsayin hanyar kawo zaman lafiya a yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi jan kunnen ne bayan sassauta kullen sa’o’i 24 da ya sa karamar hukumar Jos ta arewa sakamakon kashe mutane 37 a wuraren Yelwa Zangam dake Jos ta arewa.
Lalong ya ce farmakin karamar hukumar abu ne mai razanarwa da kuma tunatar da abubuwan takaici da suka faru a baya wadanda aka kusa mantawa dasu.
"Ku kula da yankunan ku saboda gwamnati ba za ta amince da karya doka ba a bisa ko wanne dalili saboda mulkinmu ya yi iyakar kokarin ganin ya kawo tsaro na tsawon shekaru 6 da suka gabata,” a cewarsa.
Sannan OPSH, rundunar dake kwantar da tarzoma a Filato da wasu bangarori na jihar Bauchi da Kaduna sun kori duk wani tsoro na batun wasu mutane masu kayan sojoni fa suka taru a Dutse Kura.
Dokar hana fita na awanni 24: Mazauna Jos sun koka kan karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki
Jami’in labarai, Major Ishaku Takwa ya tattauna da manema labarai a yankin inda ya ce sun zagaye ko ina amma ba su ga ko makami guda daya ba.
A cewarsa,
“Rundunar ta isa Dutsen Kura kuma ta hada kai da shugabannin anguwanni inda suka bincike ko ina sannan suka tabbatar babu wani makami ko ‘yan ta’adda a yankin.
“Sannan OPSH sun kara rike wuta wurin ganin kawo karshen duk wasu ayyukan ta’addanci a jihar Filato.”
Takwa ya kara rokon mazauna yankin a kan su cigaba da samar da labarai da bai wa jami’an OPSH hadin kai don ba za su taba barin su kaskanta ba, kuma za su cigaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin mazauna jihar.
Akwai yuwuwar 'yan bindigan da suka addabi arewa maso yamma ba 'yan kasa bane, Malamin Kirista
A wani labari na daban, a ranar Litinin, Bishop Martin Uzukwuo, wani babban Bishop da ke Minna ya lura da cewa yawancin ‘yan ta’addan da suke addabar Najeriya ‘yan kasar waje ne.
Matasan Jos sun kwace gawawwakin mutanen da aka kashe daga asibiti, sun kai ofishin gwamna da majalisa
Uzukwuo ya bayyana hakan ne a wata hira da NAN tayi dashi a Minna, Daily Nigerian ta wallafa.
Ya ce, a fatattaki duk wani dan kasar waje da ke zaune a Najeriya babu takardun da suka dace don samun zaman lafiya, Daily Nigerian ta wallafa.
Asali: Legit.ng