Akwai yuwuwar 'yan bindigan da suka addabi arewa maso yamma ba 'yan kasa bane, Malamin Kirista

Akwai yuwuwar 'yan bindigan da suka addabi arewa maso yamma ba 'yan kasa bane, Malamin Kirista

  • Bishop Martin Uzukwuo, wani babban Bishop da ke Minna, ya lura da cewa yawancin ‘yan ta’addan da ke addabar arewa maso yamma yawanci ba ‘yan Najeriya ba ne
  • Ya bayyana wannan fahimtar tasa ne a wata tattaunawa da aka yi da shi inda yace ya kamata gwamnati ta fatattake su zuwa kasashen su
  • Kamar yadda ya shawarci gwamnati, ya ce matsawar suna son zaman lafiya ya wanzu a kori duk wani dan kasar waje dake zaune a kasar nan da ba takardu

Minna, Niger - A ranar Litinin, Bishop Martin Uzukwuo, wani babban Bishop da ke Minna ya lura da cewa yawancin ‘yan ta’addan da suke addabar Najeriya ‘yan kasar waje ne.

Uzukwuo ya bayyana hakan ne a wata hira da NAN tayi dashi a Minna, Daily Nigerian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

A cewarsa ya kamata gwamnatin tarayya ta kwashe duk wadanda suke da alhakin addabar kasar nan ta mayar da su kasashensu.

Akwai yuwuwar 'yan bindigan da suka addabi arewa maso yamma ba 'yan kasa bane, Malamin Kirista
Akwai yuwuwar 'yan bindigan da suka addabi arewa maso yamma ba 'yan kasa bane, Malamin Kirista. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce, a fatattaki duk wani dan kasar waje da ke zaune a Najeriya babu takardun da suka dace don samun zaman lafiya, Daily Nigerian ta wallafa.

Uzukwuo ya tunatar da lokacin da shugaban kasa Shehu Shagari ya mayar da duk ‘yan kasar Ghana zuwa kasar su.

Ya bayyana yadda ta’addanci ya fi yawaita a kananun hukumomin da suke makwabtaka da kasar nan a arewa maso yamma inda yace manyan kalubale ne ga Najeriya.

Kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da sunan ta’addanci da garkuwa da mutane ya dade yana aukuwa, kuma za a cigaba da kashe rayuka ana lalata dukiyoyi indai ba a yi wa abin garanbawul ba.

Kara karanta wannan

Abinda yasa ƴan Najeriya ke kwana da yunwa duk da noman abinci da ake yi, Nanono

Ya kamata jami’an tsaro su kawo duk wadanda suke zargin suna da hannu a cikin lamarin nan daga nan tsoron Allah zai kama mutane da dama kuma zaman lafiya ya auku a kasar nan.
Ina rokon ‘yan Najeriya da su taimaka wa jami’an tsaro da labarai masu amfani wadanda za su taimaka musu wurin kamo duk wasu ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane don a yanke musu hukunci.
Ya kamata a dakatar da duk wasu matsalolin ta’addanci da garkuwa da mutane don kasar nan ta bunkasa, ta daukaka a idon duniya,” a cewar sa.

CJN Tanko ya yi kiran gaggawa ga wasu alkalai 6 kan hukuncin da suka zartar a rikicin PDP

A wani labari na daban, shugaban alkalan Najeriya (CJN), Justice Tanko Muhammad ya tattaro manyan alkalan jihar River, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan ya biyo bayan hukuci mabanbanta da ko wannensu ya yanke a jiharsa masu karo da juna.

Kara karanta wannan

Buhari ya yiwa 'yan bindiga masu AK-47 abun da ya fi ayyana su a matsayin 'yan ta'adda muni, Garba Shehu

A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna dangane da rikicin da ya barko jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng