Matasan Jos sun kwace gawawwakin mutanen da aka kashe daga asibiti, sun kai ofishin gwamna da majalisa

Matasan Jos sun kwace gawawwakin mutanen da aka kashe daga asibiti, sun kai ofishin gwamna da majalisa

  • Da alamun matasan Jos sun yi watsi da umurnin dokar ta bacin da gwamna Lalong ya sa
  • Wasu fusatattun matasa sun kai gawawwakin wadanda aka kashe ofishin gwamnan
  • Hakazalika sun kai gawawwakin majalisar dokokin jihar

Plateau - Garin Jos a ranar Laraba babu lafiya sakamakon kisan mutane kimanin 35 da wasu yan tada zaune tsaye suka yi a garin Yelwa Zangam, karamar hukumar Jos ta Arewa.

A cewar ChannelsTV, wasu fusatattun matasa sun garzaya asibitin Specialist dake Jos inda aka ajiye gawawwakin wadanda aka kashe kuma suka kwashe suka zuba cikin mota.

Daga nan suka garzaya majalisar dokokin jihar domin nunawa yan majalisan gawawwakin al'ummar da aka hallaka.

Duk da jawabin da kakakin majalisan ya musu don kwantar musu da hankali, matasan basu gamsu ba, sai suka garzaya ofishin gwamnan jihar kuma suka zuba gawawwakin a kasa.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

Matasan Jos sun kwace gawawwakin mutanen da aka kashe daga asibiti
Matasan Jos sun kwace gawawwakin mutanen da aka kashe daga asibiti, sun kai ofishin gwamna da majalisa Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani hali ake ciki yanzu?

Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya sake saka dokar ta baci a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Sakataren yada labaran gwamnan, Makut Simon Macham, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba.

Yace dokar za ta fara aiki ne daga karfe 4 na yamma har zuwa lokacin da hali yayi.

Gwamnan jihar ya tabbatar da wannan hari kuma yayi Allah wadai da wannan hari.

Ya yi kira ga al'ummar garin su kwantar da hankulansu.

Wani mataki gwamnan ya dauka?

A ranar Talata, Gwamna Lalong ya kaiwa shugaba Buhari ziyarar gaggawa domin sanar da shi halin da jiharsa ke ciki.

Shugaban kasa ya saurari bayanai kan kisan gillan da a kaiwa musulmi a Jos a rikicin da suka biyo baya ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamnan Plateau ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana

Bayan sauraron inda aka kwana game da lamarin, shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya ta hanyar ma'aikatar jin kai da walwala, zata tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel