Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti, sun kai wa likitoci da marasa lafiya farmaki

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti, sun kai wa likitoci da marasa lafiya farmaki

  • Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu fashi da makamai ne sun kai hari asibitin gwamnati na jihar Bayelsa a ranar Talata
  • Sakamakon harin, sun sace duk wasu kudade da tsadaddun abubuwan likitocin da suke kan aiki da na marasa lafiya
  • Ana zargin ‘yan fashin sun shiga asibitin ne bayan sun fasa katangar asibitin ta baya sannan wani jami’in tsaron asibitin ya ce wannan ne hari na biyu

Bayelsa - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai farmaki asibitin gwamnati na jihar Bayelsa, Diete Koki Memorial Hospital, inda suka sace duk wasu kudade da tsadaddun abubuwan likitoci da marasa lafiya.

Asibitin yana kan titin Opolo ne a Yenagoa, babban birnin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

Lamarin ya faru ne da safiyar Talata. Ana zargin ‘yan fashin sun fasa katangar bayan asibitin ne sannan suka shiga ciki.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti, sun kai wwa likitoci da marasa lafiya farmaki
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti, sun kai wwa likitoci da marasa lafiya farmaki
Asali: Original

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, daya daga cikin likitocin da suke kan aiki, Dr Okeleghel Awudumapu, ya sanar da manema labarai cewa ‘yan fashin sun kai farmakin ne lokacin yana dakin likitoci.

A cewarsa, sai da suka kwashe masa duk wasu kayan tagomashi da kuma na marasa lafiya sannan suka tsere.

Shugaban asibitin, Dr Emmanuel Fetepigi, bayyana aikin a matsayin kauyanci.

A cewar Dr Fetegi, hukumar asibitin da ma’aikatar lafiya ta kasa za su tabbatar sun yi iyakar kokarin ganin irin wannan lamarin bai sake aukuwa ba.

Wani jami’in tsaron asibitin, Mr James Benini, ya ce wannan shine karo na biyu da aka taba kai wa asibitin farmaki.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 3 yayin da suka kai musu farmaki kan hanyarsu ta kai masu laifi gidan yari

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya yi tsokaci dangane da lamarin ya ce:

Har yanzu ba a kawo mana rahoto ba. Amma na tura DPO Ekeki don ya nemo bayanai a kan lamarin daga asibitin.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel