Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

  • Jami'an kwastam sun cafke wata mota dauke da makamai a jihar Legas
  • An kama motar ne dauke da bindiga da kuma daurin harsashi yayin binciken tantancewa
  • An mika motar ga sashin tsaro na hukumar ta kwastam yayin da ake jiran sabon umarni

Legas - Rundunar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta Yankin Tincan, ta kwato bindiga da magazine na bindiga a boye a cikin wata motar Toyota Camry, in ji rahoton Daily Nigerian.

Kwanturolan yankin, Musa Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Legas ranar Lahadi 29 ga watan Agusta ta hannun Uche Ejesieme, jami’in hulda da jama’a na rundunar.

A cewarsa, jami'ansu dake aikin sintiri na yau da kullun a ranar 28 ga Agusta, sun yi tuntube da bindiga tare da daurin harsasanta a cikin motar Toyota Camry a wurin fita.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

Jami'an kwastam sun cafke wata mota da aka shigo da ita dauke da makamai
Jami'an hukumar kwastam | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

“Sakamakon haka kuma daidai da tsarin aikinmu (SOP), an gayyaci DSS, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro zuwa wurin.
"Bayan haka, an kai kayan sashen tsaro na hukumar kwastam domin samun cikakken adana, yayin da ake jiran rahoto zuwa hedikwatar kwastam a ranar Litinin don daukar umarni na gaba."

Mista Abdullahi ya yi amfani da wannan damar ya shawarci masu shigo da kaya ko wakilansu da su guji shiga cikin irin wannan barna, musamman abubuwa irin wannan dake cikin jerin haramtattun kayayyaki.

Ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin don bankado wadanda ke da hannu cikin lamarin tare da tabbatar da datse sarkar samar da harantattun kayayyaki.

Hukumar kwastam ta mika gurbattun magunguna na miliyoyi da ta kwata ga NAFDAC

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

A jihar Kaduna kuwa, Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, ta karbi kayayyakin magunguna marasa rajista da darajarsu ta kai Naira miliyan 100 da Hukumar Kwastan ta kama.

Kwanturola a sashin B na sashin ayyukan kwastam na tarayya, Al-Bashir Hamisu ne ya mika kayayyakin ga NAFDAC a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Hamisu ya ce rukunin masu sintiri na kan iyakokin kwastam sun kwace kayayyakin magungunan ne a watan Agusta.

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

A wani labarin, 'Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a kauyen Makoro Iri dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A cewar wani rahoton tsaro, 'yan bindigar sun mamaye kauyen inda suka harbe mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Gideon Mumini da Barnabas Ezra, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi 29 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel