Kano: An Saka Dokar Haramta Zancen Dare Tsakanin Samari Da Ƴan Mata a Wata Ƙaramar Hukuma

Kano: An Saka Dokar Haramta Zancen Dare Tsakanin Samari Da Ƴan Mata a Wata Ƙaramar Hukuma

  • An saka dokar hana yin zancen dare tsakanin samari da 'yan mata a karamar hukumar Rano ta jihar Kano
  • Tuni dai an umurci 'yan Hisbah da sauran jami'an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana saba sabuwar dokar
  • Shugaban karamar hukumar tare da mahukunta sun saka dokar ne don dakile badalar da ake aikatawa tsakanin mata da maza yayin zancen dare

Rano, Jihar Kano - Karamar hukumar Rano a Jihar Kano, a ranar Laraba ta amince da kafa dokar hana tadi ko haduwa tsakanin samari da 'yan mata da dare a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Karamar hukumar ta ce an saka wannan dokar ne saboda samun yaduwar badala da ake aikatawa tsakanin samari da yan mata har ma da zaurawa a yankin.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Jihar Kaduna ta kwashe dalibai 'yan jiharta dake karatu a jihar Filato

Mahukunta sun saka dokar haramta zancen dare tsakanin samari da 'yan mata a Kano
Taswirar Jihar Kano: Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar rahoton na Premium Times, karamar hukumar ta ce daga yanzu masoya suna iya haduwa ne kawai da rana domin yin tadi.

A cewar jami'in watsa labarai na karamar hukumar, Habibu Faragai, shugaban karamar hukumar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar ne yayin taron tsaro da masu sarautun gargajiya da mazauna garin suka hallarta.

Mr Muhammad ya ce kwamitin ta tattauna game da karuwar ayyukan badala a karamar hukumar, ya kara da cewa hakan ne yayi sanadin kafa sabuwar dokar.

Dalilin saka dakar hana zancen daren?

Ya ce an kafa dokar ne domin tsaftace karamar hukumar daga ayyukan badala da ake aikatawa cikin dare tsakanin maza da mata.

Shugaban karamar hukumar ya umurci Hukumar Hisbah da sauran hukumomin tsaro a karamar hukumar su tabbatar ana bin dokar tare da kama wadanda suka saba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamnan Plateau ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana

Kazalika, Hakimin Rano, Mannir Tafida-Abubakar, ya yi kira ga mazauna kauyen da dagatai da masu unguwanni da limamai su tabbatar mutane suna bin dokar.

Mr Tafida-Abubakar ya ce akwai kimanin manyan abubuwa uku masu alaka da tabarbarewar tarbiyya da ke ciwa mutanen garin tuwo a kwarya.

Basaraken ya ce:

"Mafi yawancin iyaye sun yi na'am da dokar kuma suna goyon baya. Idan iyaye ba su bada hadin kai ba, kuma wadannan abubuwan suka sake faruwa, kowa zai ga sakamakon sakacin."

Gwamnatin Jihar ta hana mata da maza hawa adaidaita sahu na haya guda daya tun shekarar 2019.

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Hakan yasa kotun ta bawa hukumar Hishah na jihar umurnin shirya daurin auren kamar yadda rahoton na Premium Times ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel