Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

  • Kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia, Jigawa ta aurar da yaya da ƙanwa ba da son mahaifinsu ba
  • Wata gidauniya mai kare hakkin mata da yara ne ta yi ƙarar mahaifin da ya ƙi aurar da ya'yansa mata su biyu
  • Kotun ta umurci hukumar Hisbah na jihar ta aurar da matan biyu bayan mahaifin ya ƙi amincewa da mazan da suka kawo kuma ya ƙi haɗa su da wasu mazan

Jihar Jigawa - Wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Jigawa: Kotun Shari'ar Musulunci ta aurar da yaya da ƙanwa duk da rashin amincewar mahaifinsu
Yan uwa da abokan arziki da suka hallarci daurin auren a ofishin Hisbah. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan yasa kotun ta bawa hukumar Hishah na jihar umurnin shirya daurin auren kamar yadda rahoton na Premium Times ya bayyana.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Jigawa: Kotun Shari'ar Musulunci ta aurar da yaya da ƙanwa duk da rashin amincewar mahaifinsu
Abubakar Yusuf da Amayarsa Hafsat. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Mrs Kailanini ta ce gidauniyarta ta tuntunbi Mr Malammadori sau da dama kan ya amince ya aurar da yaransa amma ya yi kunen ƙashi.

Ta ce baya da ƙin amincewar da mazajen da ƴaƴansa suka kawo, Mr Malammadori ya gaza samarwa yaran wasu mazan auren daban, duk da sun haura shekaru 30.

Jigawa: Kotun Shari'ar Musulunci ta aurar da yaya da ƙanwa duk da rashin amincewar mahaifinsu
Yusuf da Amaryarsa Khadijat. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

A ina aka daura auren matan biyu?

Kwamandan Hishah na Jihar, Ibrahim Ɗahiru, wanda ya bada auren matan biyu, ya ce mazajensu sun biya sadaki N50,000 kan kowanne mace.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Tare Motar Kuɗi, Sunyi Awon Gaba Da Muƙuden Kuɗaɗe Bayan Kashe Ɗan Sanda Da Direban Motar

Mr Ɗahiru ya ce kotun da Hisbah sun shiga lamarin ne don kare matan daga wuce gona da iri na mahaifinsu.

Jami'in na Hisbah ya shawarci ma'auratar su cigaba da girmama mahaifin nasu duk da rashin jituwar da ya shiga tsakaninsu.

Ƴan uwa da abokan arziki sun hallarci auren da aka ɗaura a ofishin Hisbah.

An aurar da matar ga Sadiq Abdulra'uf da Abubakar Yusuf a bikin da aka gudanar a ofishin Hisbah da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ba a dai samu ji ta bakin mahaifin ba kan dalilin da yasa ya ƙi aurar da ƴaƴansa biyu kuma ya gaza samar musu maza da kansa.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kutsa gidan sakataren NASIEC cikin dare sun sace shi

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel