'Yan sanda sun samo kawunan mutane 3 a firinjin ɗan wasan ƙwallo da mai sharhin wasanni

'Yan sanda sun samo kawunan mutane 3 a firinjin ɗan wasan ƙwallo da mai sharhin wasanni

  • ‘Yan sandan kasar Ghana sun damki wani sanannen dan kwallo, Richard Gyamfi wanda aka fi sani da Fire Man da kawunan mutane 3 a firinjinsa
  • Bayan bayyanar lamarin ne, wani mutum da ya rasa dan sa yace dan kwallon ya yaudari dan sa mai shekaru 13 inda ya kai shi dakin shi ya kashe shi
  • Kamar yadda abokansa da suka je filin kwallon tare suka tabbatar, sun gan shi tare da Fire Man, bayan ya musa ne aka balle kofarsa aka ga gawar

Ghana - Hukumar ‘yan sandan kasar Ghana sun kama wani dan kwallon kafa, Richard Gyamfi wanda aka fi sani da Fire Man da kawunan mutane 3 a firinjinsa a wuraren Sunyami, shafin Linda Ikjei ya ruwaito.

Gidan rediyon Sky FM dake Sunyami sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka ce mahaifin daya daga cikin mamatan, Mr Thomas Aygei ya bayyana yadda wanda ake zargin ya yaudari dansa, Louis Agyemang Junior mai shekaru 13, a filin kwallo da ke Sunyami Abesum har dakinsa inda ya hallakasa.

'Yan sanda sun samo kawunan mutane 3 a firjin dan wasan kwallo da mai sharhin wasanni
'Yan sanda sun samo kawunan mutane 3 a firjin dan wasan kwallo da mai sharhin wasanni. Hoto daga Linda Ikeji
Asali: Facebook

Yaro mai shekaru 13 ya bar gida, bai koma ba

Da yake tagwaye ne yaron da dan uwansa, mamacin ya bar gida zai tafi filin kwallon. Daya daga cikin abokan mamacin, mai suna Tweneboa sun tabbatar wa da mahaifin cewa sun gan shi tare da Fire Man.

An fara zargin Gyamfi tun bayan ya musanta ganin yaron bayan an fuskance shi da maganar, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

An balle kofar dakin Gyamfi domin bincike

Bayan iyayen yaron sun kai wa dan kwallon ziyara gidansa sun tarar dashi a kulle. Bayan an balle kofar ne aka ga gawar Louis Agyemang Junior a kwance an cire masa kai.

Wanda ake zargin ya sha gwale-gwale kafin aka mika shi ga ofishin ‘yan sanda dake Sunyami Abesim. Bayan ‘yan sanda sun duba duka dakin sa, sun ga gawa a cikin buhu sannan sun ga kawunan mutane uku ciki har da na Louis Agyemang.

‘Yan sandan Abesim sun mika shi zuwa ofishin ‘yan sanda na yankin Borno don cigaba da bincike.

Yanzu haka kawunan guda uku ciki har na Louis Agyemang Junior suna ma’adanar gawa ta Best Care dake kudancin Sunyani.

Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna

A wani labari na daban, tsohon kwararren dan jarida mazaunin Kaduna, Muhammadu Dan Tankon Sa'i ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tankon Sa'i ya rasu ne a ranar Lahadi 22 ga watan Agusta bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin tsohon ma'aikaci ne a gidan rediyon jihar Kaduna wato Kaduna State Media Corporation (KSMC).

Asali: Legit.ng

Online view pixel