Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna

Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna

  • Tsohon dan jarida mazaunin Kaduna, Muhammadu Dan Tankon Sa'i ya kwanta dama
  • Marigayi Tankon Sa'i ya rasu ne a Kaduna bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Tankon Sa'i ya yi aiki da BBC a shekarun 1970s kana daga bisani ya koma aiki da KSMC

Jihar Kaduna - Tsohon kwararren dan jarida mazaunin Kaduna, Muhammadu Dan Tankon Sa'i ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tankon Sa'i ya rasu ne a ranar Lahadi 22 ga watan Agusta bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna
Allah ya yi wa tsohon ɗan jarida, Tankon Sa'i, rasuwa a Kaduna
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayin tsohon ma'aikaci ne a gidan rediyon jihar Kaduna wato Kaduna State Media Corporation (KSMC).

Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa

Wani daga cikin iyalansa da ya sanar da rasuwarsa, ya bayyana marigayin a matsayin tsohon dan jarida, wanda ya kayyatar da nishadantar da masu sauraren rediyo da shirye-shiryensa na labaran Hausa da wasu shirye-shiryen tun daga shekarun 1960s.

Majiyar ya ce:

"Marigayin tsohon ma'aikaci ne na Kamfanin Watsa Labarai na Birtaniya, (BBC) a shekarun 1970s, kuma dimbin masu sauraronsa za su yi kewansa.
"Muna addu'ar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya saka masa da gidan aljanna Firdausi, ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa."

Rahoton na Daily Trust ya ce an birne marigayin bayan yi masa sallar jana'iza a masallacin rukunin gidajen Kwallejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel