Ana cigaba da yi wa musulmi kisar mumuƙe a Plateau, Ƙungiyar NCMPI ta koka

Ana cigaba da yi wa musulmi kisar mumuƙe a Plateau, Ƙungiyar NCMPI ta koka

  • Shugaban kungiyar samar da zaman lafiyan musulmai na arewa ta tsakiya, Alhaji Saleh Zazzaga ya koka akan kisan da aka cigaba da yi a jihar Filato
  • Ya bukaci jami’an tsaro da su sanya ido matuka kuma su tabbatar sun cigaba da kulawa da dukiya da rayukan jama’an jihar wacce take da iyaka da Kaduna ta kudu
  • Ya roki jami’an tsaro akan mayar da hankulansu wuraren Jos zuwa Bukuru don gudun bata-gari su cigaba da kaiwa mutanen da basu ji ba basu gani ba hari

Jos, Filato - Shugaban kungiyar samar da zaman lafiyan musulmai na arewa ta tsakiya (NCMPI), Alhaji Saleh Zazzaga ya koka a kan kisan gillar da ake cigaba da yi a wasu wurare a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Roƙi Jama’a Su Rungumi Tubabbun Ƴan Boko Haram, a Kuma Koya Musu Sana’a

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya roki jami’an tsaro a kan su mayar da hankulansu kacokan kuma su tabbatar sun cigaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin jama’a mazauna garuruwan da suke da iyaka da kudancin jihar Kaduna.

Ana cigaba da yi wa musulmi kisar mumuƙe a Plateau, Ƙungiyar NCMPI ta koka
Ana cigaba da yi wa musulmi kisar mumuƙe a Plateau, Ƙungiyar NCMPI ta koka. Hoto dafa Daily Trust
Asali: Facebook

Zazzaga ya yi bayani dalla-dalla

A wata hira da manema labarai sukayi da Zazzaga a ranar Juma’a, ya ce shugabannin addinai na musulunci da kirista su mike suyi iyakar kokarin ganin su janyo hankalin jama’a don dawo da zaman lafiya saboda mabiyansa suna bin duk abubuwan da suka ce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya roki jami’an tsaro akan su mayar da hankulansu wuraren Jos zuwa Bukuru yadda bata-gari za su daina cigaba da kaiwa mutanen da basu ji ba basu gani ba hari, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yabawa yadda gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya tsaya tsayin-daka wurin kama bakin zaren da kuma daukar tsauraran matakai a kan dakatar da rikicin wanda idan banda sa bakinsa da yanzu al’amarin ya faskara.

Kara karanta wannan

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

Zazzaga ya yi kira ga shugabannin gargajiya da mazauna yankuna da suyi gaggawar bayyana masu daukar doka a hannunsu a anguwanninsu saboda jami’an tsaro su kawo dauki.

Kaman Dirama: Yadda Ƴan Sanda Suka Sha Mugun Duka a Hannun Ƴan Banga Saboda Ganyen Wiwi

A wani labari na daban, kungiyar Edo Security Network ta yan banga a jihar, ta kama yan sanda biyu kan zargin samunsu da wani ganye da ake zargin wiwi ne a jihar ta Edo, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan banga sun kama yan sandan ne a Oko-Ogba a hanyar zuwa filin tashin jiragen sama da ke Benin, babban birnin jihar yayin wani bincike da suke yi a hanyar.

Yan bangan sun bincika mota kirar Lexus mai rajista RX330 ne da daya daga cikin yan sandan ke tukawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164