Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?
- Akwai kokwanton cewa yawancin wadanda suke zubar da makamansu gaban sojoji ba asalin mayakan Boko Haram bane kawai wasu mutanen ne daban
- Akwai wadanda suka yarda da cewa wasunsu basu da yadda za su yi ne, saboda kuncin rayuwa da walhalu shiyasa suka tuba don su mori tagomashin gwamnati
- Sai dai darektan yada labaran soji, Manjo Janar Olufemi Sawyer, ya musanta wadannan maganganun inda yace duk soki burutsu jama’a suke yi, karatun tsuntsaye
Borno - Jama’a da dama sun yi ta kokwanto akan tubabbun mayakan Boko Haram har wasu suna cewa da kyar idan da gaske su din ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wasu kuma sun fi yarda da cewa wasunsu da suka dauki makamai suna yakar anguwanni da jama’an jiha sun mika wuya ne kawai don karfinsu ya kare kuma basu da wata mafita da ta wuce su shiga sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta bude na yafiya don su mori tagomashi.
Me rundunar sojin Najeriya tace a kan wannan zargin?
Sai dai a ranar Laraba aka tuntubi darektan yada labaran soji, Manjo janar Olufemi Sawyer inda ya musanta duk wadannan maganganun yace ya kamata ‘yan Najeriya su rage yada jita-jita.
Ya musanta kin amincewa da tubabbun ‘yan Boko Haram din inda yace idan ba su bane ta ya za a yi sojoji su ga matan Chibok din da aka sata har sun auri mayakan sun haihu tsawon shekaru 7.
Janar Sawyer ya tunatar akan dokokin kasa da kasa na yaki inda yace:
Akwai dokoki idan mayakin ta'addanci yana so ya mika wuya... Ba za a iya kashesshi ba.
Me majiyoyi masu kusanci da filin daga suka ce?
Akwai majiyoyi wadanda suke kusa da filin dagar a arewa maso gabas inda suka ce kadan daga cikin mayakan ne suka yi tubar hakika kuma suka shirya canja rayuwa don su cigaba da harkoki kamar kowa.
A cewarsu, akwai bukatar a kula kwarai akan harkar tsaron arewa maso gabas musamman akan amsar tubabbun mayakan Boko Haram saboda wasun su basu da gaskiya.
Daily Trust ta tattaro bayanai akan yadda babu wasu manyan kwamandojin ISWAP da suka tuba suka mika wuyansu ga jami’an tsaro musamman a Borno.
Akwai rahotanni akan yadda wadanda aka tursasa wa kuma aka ragargaza ne kadai da matansu da yaransu suka mika wuya. Fiye da mutane 1000 sun zubar da makamansu ga sojoji a Bama, Gwoza, Mafa da Konduga da sauran wurare dake kudanci da tsakiyar Borno.
Sansanoninsu suna dajin Sambisa kusa da dutsen Mandara kuma dama yawancinsu mazauna wurin ne tun kafin bayyanar Boko Haram. Wasunsu gamsar dasu aka yi da hujjoji suka shiga akidar yayin da wasunsu kuma da makamai aka tankwasa su.
Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba
A wani labari na daban, mayakan ISWAP na Najeriya sun canja tsarin shugabancinsu da kungiyar masu basu shawarwari akan yadda mayakan Boko Haram da dama suka zubar da makamansu ga sojojin Najeriya.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, an tumbuke shugabannin ne bisa umarnin hedkwatar ISIS na Iraq da Syria, bisa kasa tabbatar da hadin kan ISWAP da mayakan Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau.
Asali: Legit.ng