Kaman Dirama: Yadda Ƴan Sanda Suka Sha Mugun Duka a Hannun Ƴan Banga Saboda Ganyen Wiwi

Kaman Dirama: Yadda Ƴan Sanda Suka Sha Mugun Duka a Hannun Ƴan Banga Saboda Ganyen Wiwi

  • Rundunar yan sanda ta yi tsokaci game da tsare jami'anta da dukansu da yan banga suka yi kan ganyen wiwi
  • Rundunar yan sandan ta ce babu shakka shugaban yan bangan da yan kungiyarsa sun san cewa motar da aka ga wiwi din ba na yan sandan bane
  • Yan sandan biyu sun tafi ofishin yan bangan ne domin neman wani mutum da aka tsare amma sai yan bangan suka lakada musu duka

Jihar Edo - Kungiyar Edo Security Network ta yan banga a jihar, ta kama yan sanda biyu kan zargin samunsu da wani ganye da ake zargin wiwi ne a jihar ta Edo, Daily Trust ta ruwaito.

Yan banga sun kama yan sandan ne a Oko-Ogba a hanyar zuwa filin tashin jiragen sama da ke Benin, babban birnin jihar yayin wani bincike da suke yi a hanyar.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Kaman Dirama: Yadda Ƴan Sanda Sun Sha Mugun Duka a Hannun Ƴan Banga Saboda Ganyen Wiwi
Kwamishinan Yan Sandan Jihar Edo, CP Philip Ogbadu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bangan sun bincika mota kirar Lexus mai rajista RX330 ne da daya daga cikin yan sandan ke tukawa.

A wani bidiyo, daya daga cikin yan sandan wanda aka saka wa ankwa, ya amsa cewa haramtaciyar kwayar ne ke cikin motan sai dai ya ce sun kwato ne daga hannun wasu wadanda ake zargi da laifi, The Punch ta ruwaito.

Shugaban yan banga, John Osasere Ohonba, ya ce ba an yi kamen bane domin bata wa yan sanda suna sai dai domin tabbatar da tsaro a yankin.

A bangarensa, kakakin yan sanda na jihar Edo, SP Bello Kotongs ya zargi yan bangan da kaiwa jami'ansu hari.

Ya ce yan sandan ba su da laifi a maimakon yadda yan bangan ke neman nuna wa mutane.

A cewarsa:

"An saka wa yan sandan ankwa babu tare da wani dalili na hakika ba, an doke su, hakan yasa an kwantar da su a asibiti - domin raunin da suka samu.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da ‘yan bindiga suka harbe sojoji 7 har lahira a Katsina

"Ainihin abin da ya faru shine yan sandan biyu sun tafi ofishin yan bangan da wani Lucky da budurwarsa suna neman wani Ikpefua Idowu, wanda John Osasere Ohonba da aka fi sani da Awilo da yaransa suka kama.
"Babu tantama cewa Mr Awilo da yaransu sun san cewa motar Lexus RX330 da ke bidiyon ta Lucky ce, dan uwan Ikpefua Idowu wanda Awilo da yaransa suka kama kuma yan sandan suka tafi nema.
"Duk da cewa yan sandan sun bayyana ko su wanene kuma Awilo da yan kungiyarsa sun fahimci hakan, ana iya gani a bidiyon cewa Awilo sanya da riga mai jan launi shine ya fara kai musu duka."

Bello ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar Edo, Philip Ogbadu ya umurci a yi bincike kan lamarin.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel