Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Roƙi Jama’a Su Rungumi Tubabbun Ƴan Boko Haram, a Kuma Koya Musu Sana’a

Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Roƙi Jama’a Su Rungumi Tubabbun Ƴan Boko Haram, a Kuma Koya Musu Sana’a

  • Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) tayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya akan shiryawa da tubabbun ‘yan Boko Haram da mayakan ISWAP
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata takarda wacce ta saki a ranar Alhamis inda tace ya kamata a kyautata musu tamkar ‘yan uwan da suka bata aka tsincesu yanzu
  • MURIC ta bukaci a koya musu sana’o’i don su samu sababbin hanyoyin da za su cigaba da kulawa da iyalansu da kawunansu nan gaba

Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC tayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya akan shiryawa da tubabbun mayakan Boko Haram da ISWAP.

News Wire NGR ta ruwaito cewa, MURIC ta bayar da wannan shawarar ne a wata takarda da ta saki a ranar Alhamis inda tace ya kamata a kula da tubabbun ‘yan ta’addan tamkar ‘yan uwa wadanda suka bata aka gansu.

Kara karanta wannan

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

MURIC ta Bukaci FG da Jama'a da su Rungumi Tubabbun 'yan Boko Haram, a Koya Musu Sana'a
MURIC ta Bukaci FG da Jama'a da su Rungumi Tubabbun 'yan Boko Haram, a Koya Musu Sana'a. Hoto daga Newswire
Asali: Facebook

A koyar da tubabbun 'yan ta'adda sana'o'i

Ta bayar da shawarar ne inda tace ya kamata a koyar da su sana’o’i don su samu damar cigaba da kulawa da kawunansu da iyalansu nan gaba.

Kungiyar ta yi kira ga mazauna Borno da su rungumesu kuma su cigaba da mu’amala dasu.

Ta hori mutane da su guji tsangwamarsu

MURIC tace nasarar yaki a zuciyar mazaje take don haka shiryawa da tubabbun ‘yan ta’addan ne kadai hanyar da za a samu nasarar cin yakin da gaske.

Yankin arewa maso gabas a Najeriya sun fuskanci wani sauyin yanayi na tubar mayakan Boko Haram da ISWAP, wanda dubbaninsu suka zubar da makamansu. Sai kuma yankin suka samu karuwar jama’a wadanda su ne tubabbun ‘yan ta’addan.

Wannan sabon nauyi ne da ya hau kan gwamnatin jihar. Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, jiya ya roki gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya a kan su taimaki jiharsa wurin shiryawa da tubabbun mayakan.

Kara karanta wannan

Gidan Soja: Dalilin da yasa muke karbar tuban mayakan Boko Haram da suka mika wuya

MURIC tana taya hazikin Gwamna Zulum rokon FG da sojojin Najeriya da su yi iyakar kokarinsu wurin taimakawa gwamnatin jihar ta shirya dasu. Ya dace a taya gwamnan da kullum yake cikin sojoji a filin daga dare da rana yana shiga asibitoci da azuzuwa don tabbatar da ayyukan jihar suna tafiya yadda ya dace.
Mu na so mu tunatar da cewa neman shiri ya fi yaki sauki kuma ya fi kawo cigaba da zaman lafiya. Don haka FG ta tsaya tsayin daka wurin ganin an saukaka komai.
Ya kamata a zaunar da tubabbun mayakan Boko Haram da na ISWAP a koya musu sana’ar da za su amfani rayuwarsu da ta iyalansu nan gaba.
MURIC ta bukaci jama’a kada su tsangwamesu, su nuna musu soyayya. Kada su kuskura su kyamacesu.

Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai

Karu Ishaya, sakataren hukumar samar wa da mahajjatan addinin kirista walwala, CPWB, na jihar Gombe ya bayyana yadda gwamnatin jihar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin daukar nauyin mahajjatan kiristoci 70 zuwa kasar Jordan.

Kara karanta wannan

Wannan ba shine farko ba: Izala ta yi martani kan kashe Musulmai da aka yi a Jos

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ishaya ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Otal din Dead Sea Spa dake Sweimeh a Jordan yayin amsa tambayoyin manema labarai.

A cewarsa irin karamcin da gwamnatin jihar ta nunawa masu bautar ya sa su matukar farin ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel