Yanzu-Yanzu: Ƴan bindiga sun yi wa manoma 5 kisar gilla a hanyarsu na zuwa gonakinsu a Toro

Yanzu-Yanzu: Ƴan bindiga sun yi wa manoma 5 kisar gilla a hanyarsu na zuwa gonakinsu a Toro

  • Ƴan bindiga sun kashe manoma biyar a hanyarsu na zuwa gonakinsu a kauyen Toro a jihar Osun
  • Wani mazaunin garin ya tabbatar da lamarin yana mai cewa wadanda aka kashe yan asalin garin Modakeke ne
  • Rundunar yan sandan jihar Osun ta bakin kakakinta, ta ce ta samu labarin kashe mutanen kuma an tura jami'ai yankin

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mutane biyar yan asalin garin Modakeke a jihar Osun kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Ƴan bindiga sun yi wa manoma 5 kissar gilla a hanyarsu na zuwa gonakinsu a Toro
Hoton garin Modakeke ta sama. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

The Punch ta ruwaito cewa mutanen biyar suna kan hanyarsu na zuwa gonakinsu na a kauyen Toro a ranar Juma'a 20 ga watan Agusta yayin da yan bindigan suka kashe su.

Wani jagoran al'umma a Modakeke ya tabbatar da kisan

Wani jagoran al'umma a garin Modakeke mai suna Mr Femi Eluyinka, wanda ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin ya ce wasu mutanen garin da 'yan sanda sun kwashe gawarwarkin mutanen.

Mr Eluyinka ya ce kisan ya janyo zaman dar-dar a garin tare da tada hankulan mutane.

Ya ce:

"Jami'an yan sanda sun iso. Hankulan mutane ya tashi. Dukkansu biyar yan asalin garin Modakeke ne kuma an kashe su ne a safiyar yau a kan hanyar Toro. Suna hanyarsu ne zuwa gonakinsu."

Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Osun, Mr Yemisi Opalola ya ce:

"Mun samu labarin cewa an kashe wasu mutane kuma kwamishinan yan sanda ya tura karin jami'ai zuwa yankin."

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel