Da Dumi-Dumi: An sake kashe mutum 5 a wani hari a Jihar Plateau

Da Dumi-Dumi: An sake kashe mutum 5 a wani hari a Jihar Plateau

  • Yan bindiga sun halaka mutane biyar a karamar hukumar Bassa, jihar Plateau
  • Ezekiel Bini, Shugaban kungiyar Cigaban Irigwe na kasa ya tabbatar da kisan
  • Bini ya kara da cewa baya ga mutanen 5 da aka kashe, an sace wasu mutum hudu

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mutane biyar a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau kamar yadda News Wire NGR ta ruwaito.

An gano cewa an kashe mutanen biyar ne a yayin da yan bindigan suka kai hari kauyen Chando-Zrrechi (Tafi-Gana) a daren ranar Talata.

Da Dumi-Dumi: An sake kashe mutum 5 a wani hari a Jihar Plateau
An sake kashe mutum 5 a wani hari a Jihar Plateau. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar Cigaban Irigwe na kasa ya tabbatar da kisan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

News Wire NGR ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Cigaban Irigwe na kasa, Ezekiel Bini, ya tabbatar da kisan a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar ɗan sanda, matarsa da ƴaƴansu 5 a cikin gidansu

A cewarsa, kawo yanzu ana cigaba da neman wasu mutane hudu bayan yan bindigan sun kama su.

Bini ya ce:

"Eh, da gaske ne an kashe mutane biyar yanzu haka muna kan hanyarmu na zuwa ganin gwamna bisa cigaba da kashe mutane a garuruwan Bassa.
"An kai wa mutanen mu hari daren jiya (Talata) a Chando-Zrrechi an kashe mutum biyar.
"Suna zaune a gidajensu yan bindiga suka zo suka kashe su duk da dokar hana fita da gwamnati ta saka.
"An kai gawarwakinsu dakin ajiye gawa. Bayan mutane biyar din da aka kashe daren jiya, an kama wasu mutane hudu kuma har yanzu ba mu gano su ba."

A baya-bayan nan dai ana ta kai hare-hare a unguwanni a karamar hukumar Bassa da wasu kauyuka da ke wajen Jos a jihar ta Plateau.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164