Hawaye sun kwaranya yayin da ‘yan bindiga suka harbe sojoji 7 har lahira a Katsina
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina
- Miyagun sun kashe sojojin Nijar bakwai bayan da sojojin suka bi sahun 'yan fashi da suka sace dabbobi sannan suka tsallaka zuwa iyakar Najeriya
- Wani ganau ya ce tun bayan harin da aka kai a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, ba a ga wasu daga cikin sojojin ba
Jibia, Katsina - Yan bindiga sun kashe sojojin Nijar bakwai a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kai harin ne a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, a kauyen Kadobe kimanin kilomita 4 daga kauyen Kukar Babangida.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce 'yan bindigar sun hango sojojin Nijar din suna tafe bayansu sannan kuma suka kashe bakwai, The News Wire ta ruwaito.
Da yake ci gaba da magana, mazaunin garin ya bayyana cewa ba a ga wasu daga cikin sojojin cikin ba ciki har da wadanda suka yi kira da a kara musu karfi tun bayan harin.
Mazauna garuruwan da ke kan iyaka a yankunan da 'yan ta'adda suke sun dogara da sojojin Nijar don basu agaji lokacin da 'yan bindiga suka kai musu hari.
'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja
A wani labarin, mun ji cewa masu garkuwa da mutane sun harbe wani matashi, Haruna Dako, sannan sun sace kayan abinci iri-iri a Kambu dake wuraren Abaji a birnin tarayya, Abuja.
Daily Trust ta ruwaito yadda kauyen Kambu, wanda yake karkashin Chakumi yakeda iyaka da Gwagwalada, inda Rafin Gurara yake gudana tsakanin garuruwan.
Mazaunin garin mai suna Yahaya ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 10:27 na dare lokacin da masu garkuwa da mutane suka shigo garin da yawansu.
Asali: Legit.ng