Tsohon mijina ya ce ba zai iya ciyar da shida daga cikin ƴaƴan mu 9 ba, mata ta yi ƙara a kotun shari'a
- Wata mata ta yi karar tsohon mijinta tana mai cewa ya ce ba zai iya ciyar da yaransu shida da ke hannun ta ba
- Matar ta bukaci kotun shari'a ta umurci mijinta ya rika biyan jimillar N36,000 duk wata domin kulawa da yaransu shidan
- A bangarensa, tsohon mijinta ya nemi kotu ta mayar masa da yaransu shidan yana mai cewa matar ba za ta iya kula da su ba
Farira Isah, wata mata da mjinta ya sake ta, ta bukaci kotu ta umurci tsohon mijinta Abubakar Hamza ya fara daukan nauyin dawainiyar yaransu shida da ke hannun ta, The Cable ta ruwaito.
Farira ta bayyana hakan ne a kotun shari'a da ke zamansa a Magajin Gari, Jihar Kaduna a ranar Alhamis.

Asali: UGC
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan
Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa
Ta kuma shaida wa kotun cewa Hamza ya sake ta ne a ranar 3 ga watan Agusta, kuma kotu ta bata ikon rike shida cikin yaransu tara.
A cewar ta, Hamza ya ce ba zai iya daukan dawainiyar ciyar da yaransu shida da ke hannunta ba kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Farira ta kuma bukaci kotun ta hana Hamza zuwa gidanta sannan ya rika biyan N36,000 duk wata domin dawainiyar yaran shida da ke hannunta. (N6,000 ga kowanne yaro).
Ta ce:
"Hamza ya fada min ba zai iya ciyar da yaran shida ba. Ina son kotu ta umurci ya dauki dawainiyarsu ta hanyar biyan N6,000 kan kowanne yaro duk wata sannan a hana shi zuwa gida na kowanne safe da dare."
Abin da Hamza ya shaida wa kotu?
A martaninsa, Hamza, wanda aka yi kara kuma mazaunin Kaduna, ya roki kotun ta mayar masa da yaran shida da ke hannun Farira.
Ya ce:
"Ina son in rika kula da su. Uku na zaune tare da ni. Ba za ta iya kula da su yadda ya dace ba."
Matakin da alkali ya dauka?
Bayan sauraron bangarorin biyu, Murtala Nasir, alkalin kotun ya umurci wanda aka yi kara ya kawo shaidu da ke nuna cewa tsohuwar matarsa ba za ta iya kulawa da tarbiyantar da yaransu ba.
Nasir ya kuma umurci Hamza ya dena zuwa gidan tsohuwar matarsa har sai an yanke hukunci a shari'ar.
Ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Agusta.
Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa
A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.
Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.
Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng