Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa
- Kotu ta raba aure na shekara 10 saboda sata da miji ya ce matarsa ta fitine shi da shi
- Magidancin da ya yi karar matarsa a kotun ya kuma zarge ta da bin mazajen aure
- Matar bata amsa gayyatan kotu ba hakan yasa alkali ya raba auren ya ce kowa ya kama gabansa
Legas - Wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.
Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.
Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya ce:
"Dukkan zaman sauraron shari'a da aka yi, wacce aka yi kara ta ki bayyana gaban kotu duk da cewa an kai mata sammaci sau da yawa.
"Don haka, kotun bata da wani zabi sai dai raba auren.
"Kotun ta tsinke ingiyar auren da ke tsakanin Mutiu da Aliyah Bamgbose a yau.
"Daga yau, ba matsayin mata da miji ku ke ba.
"Kowa ya kama gabanasa ba tare da cin zarafin juna ba; kotu na muku fatan alheri a duk abin da za ku yi a nan gaba."
Mr Kolawole ya bawa wacce aka yi kara ikon rike yayansu tagwaye mata ya umurci Bambgose ya rika biyan N10,000 duk wata kudin abincinsu.
Ya kuma bawa wanda ya yi karar ikon rike dansu namiji.
Mata ta ta fitine ni da sata
Bamgbose ya ce: "Mata ta barauniya ce, bata taba gamsuwa da abin da na ke bata, a kullum sace min kudi ta ke yi.
"Wanda ya fi min zafi shine lokacin da ta sace min Naira miliyan 3 ta bannatar.
"Saboda halinta, na fara ajiye kudi a rufin gidanmu amma duk da haka tana shiga ta sace.
"Da na gaji sai na bude asusun ajiya a banki hakan ya fusata ta ta fara gallaza wa rayuwata.
"Bisa dukkan alamu kudi na ta ke so ba ni ba."
Mata na tana bin maza a unguwan mu
Bamgbose ya kuma zargi matarsa da bin maza masu aure a unguwarsu. Ya ce ya yi wa wasu mazajen gargadi su dena harka da ita amma bata dena ba.
Daga bisani ta kwashe kayan gidansa ta tsere da tagwayensu mata biyu da bar masa yaro na miji.
Ya kuma kara da cewa tana bin bokaye don ya taba ganin laya a gidansu kuma ta gaza yin bayyanin inda ta samo shi.
'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa
A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.
Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.
Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.
Asali: Legit.ng