Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

  • Kungiyar Taliban ta bayyana cewa, za ta dama da mata a harkokin mulkinta kamar yadda addini ya tanada
  • Taliban ta bayyana haka ne bayan da ta karbe mulkin kasar Afghanistan daga hannun Ashraf Ghani na kasar
  • A halin yanzu, Taliban ba ta fitar da wani cikakken bayani kan yadda za ta tafiyar da mulkin ba, amma za ta dama da mata

Afghanistan - Kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta sanar da yin afuwa a fadin kasar tare da kira ga mata da su shigo cikin sabuwar gwamnatinta, Aminiya ta ruwaito.

Taliban ta yi hakan ne a kokarinta na kwantar da hankula a Kabul, babban birnin kasar, inda mutane suka yi ta turmitsutsi a filin jirgin sama domin ficewa daga kasar bayan kungiyar ta hambarar da gwamnatin kasar da Amurka ke marawa baya.

Kara karanta wannan

Shugaban Afghanistan ya tsere daga kasar yayin da Taliban ke dab da shiga Kabul

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta
Mahukuntan Taliban | Hoto: reuters.com
Asali: UGC

Cikin wata sanarwar dauke hannun Enullah Samangani daga hukumar raya al'adu ta Taliban, wacce ita ce ta farko da Taliban ta fitar tun bayan hambarar mulkin shugaba Ashraf Ghani, ta ce:

“Masarutar Musulunci ta (Afghanistan) ba ta so a kuntata wa mata, muna kira da su shigo gwamnati bisa tsarin Musulunci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba a fayyace tsarin yadda gwamnati za ta kasance ba tukuna, amma kamar yadda aka saba, gwamnatin Musulunci za a yi 100 bisa 100 kuma ana bukatar kowane bangare ya shigo a dama da shi."

Sanarwar ba ta yi cikakken bayani a kan wasu batutuwa ba, amma ta ce al’ummar kasar Afghanistan Musulmi ne, sun kuma san dokokin addini da Taliban take so su kiyaye.

Ta ci gaba da cewa:

“Mutanen kasar nan Musulmi ne kuma mu ba mun zo ne domin mu tursasa su shiga Musulunci ba.”

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

A halin da ake ciki, wani jami'in Taliban ya shaida wa Reuters cewa suna duba rahotannin ficewar Ghani daga kasar.

A ranar Lahadin da ta gabata, sojojin Taliban sun kewaye fadar mulkin Afghanistan, inda suka yi alkawarin cewa Taliban ta umarci mayakanta da su guji tashin hankali tare da bayar da kariya ga duk wanda ke son barin Kabul.

Shugaban Afghanistan ya tsere daga kasar yayin da Taliban ke dab da shiga Kabul

A kasashen ketare kuwa, shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga Afghanistan yayin da Taliban ke dab da shiga birnin Kabul, a cewar babban mai shiga tsakani na zaman lafiya na kasar Abdullah Abdullah.

Abdullah, shugaban babbar majalisar sasantawa ta kasa, a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook yana cewa:

"Tsohon shugaban na Afgahnistan ya bar al'umma."

Wani babban jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Ghani ya tafi ne zuwa Tajikistan.

Kara karanta wannan

Bayan hallaka musulmai sama da 20 a Jos, gwamnati ta sanya dokar hana fita

Ficewar Ghani ta zo ne a yayin tattaunawar mika mulki cikin lumana bayan mayakan Taliban sun kewaye Kabul bayan da suka kwace manyan biranen larduna 34 na kasar cikin kasa da makonni biyu.

Indonisiya ta yi nadama kan yadda aka ci zarafin jami'in diflomasiyyar Najeriya

A wani labarin daban, Gwamnatin Indonisiya ta bayyana yin nadama da abin da ya faru da jami’in diflomasiyar Najeriya inda wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna jami’anta na shige da fice sun makure shi, BBC Hausa ta ruwaito.

Bidiyon ya nuna yadda jami’in mai suna Abdulrahman Ibrahim wasu maza sun cukuikuye shi a cikin mota.

Najeriya bayan fitar bidiyon ta nuna fushinta tare da yin Allah wadai da abin da ya faru wanda ta ce “ya saba dokar kasa da kasa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel