Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro
- Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a ranar Alhamis
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, 17 ga watan Agusta
- A yan baya-bayan nan dai hukumomin tsaro na ta samun nasara kan miyagu inda suke ta mika wuya cikin rudani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wata ganawa da shuwagabannin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Muryar Najeriya ta ruwaito cewa za su yi ganawar ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Agusta.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, jaridar Daily Post ta ruwaito.
Adesina ya ce:
"A 'yan makonnin da suka gabata jami'an tsaron sun kara kaimi wajen yaki da masu tayar da kayar baya, 'yan fashi, da duk wasu masu aikata laifuka da ke damun kasar, kuma a yanzu suna mika kansu cikin rudani.
"Za a sanar da Shugaban kasar kan abubuwan da ke faruwa a taron na ranar Alhamis, yayin da za a tsara yadda za a kawo karshen kalubalen da ke addabar kasar."
Shugaban kasar ya dawo Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata bayan ya shafe kwanaki 18 a Landan, inda ya halarci taron ilimi sannan kuma ya duba lafiyarsa.
Kisan Jos: Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami ga Sheikh Dahiru
A wani labarin, Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana cewa shugaban Muhamadu ya kasa cin abinci ranar da aka kai hari kan Musulmai a Jos.
A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan
A ziyara ta musamman da ya kaiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a madadin Buhari, Pantami yace Buhari ya yi matukar bacin rai kan abinda ya faru har abinci ya gaza ci.
Yace:
"Bayan abin ya faru kuma da gaggawa shi Shugaban kasa tun a ranar ya bada umurni wa jami'an tsaro ayi bincike akai kuma wadanda aka kamasu da laifi a kaisu kotu kuma a hukuntasu."
"Ya yi magana da manyan jami'an gwamnati na tsaro a kai. Ya dawo daga tafiya tsakani da Allah da abin ya faru abinci ma yaci gagara yayi."
Asali: Legit.ng