Dansadau: Akwai wadanda ba 'yan Najeriya ba cikin sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Zamfara

Dansadau: Akwai wadanda ba 'yan Najeriya ba cikin sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Zamfara

  • Sanata Saidu Dansadau ya ce wasu daga cikin ‘yan ta’addan da suka isa kudancin masarautar Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara ‘yan kasashen ketare ne
  • A wata tattaunawa da aka yi da Dansadau, ya ce ‘yan bindigan da ake zargin mayakan ISWAP ne sun fara yada zangonsu a wani daji dake kusa da Dansadau suna fatattakar ‘yan bindiga
  • Ya ce suna yin hakan ne don su soyu a zuciyar mazauna yankin don su samu tudun rabewa daga nan su addabi kowa don yanzu haka ‘yan bindigan dake nan ma tsoronsu suke ji

Zamfara - Sanata Saidu Dansadau ya ce wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka isa kudancin masarautar dake karamar hukumar Maru ba asalin ‘yan Najeriya bane.

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka koma yi wa sauran ‘yan bindiga wa’azi a kan su daina kai wa makwabtansu farmaki.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulunci Ta MURIC Ta Roƙi Jama’a Su Rungumi Tubabbun Ƴan Boko Haram, a Kuma Koya Musu Sana’a

Dansadau: Akwai wadanda ba 'yan Najeriya ba cikin sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Zamfara
Dansadau: Akwai wadanda ba 'yan Najeriya ba cikin sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sanata Dansadau ya fallasa sabbin 'yan ta'adda

A wata tattaunawa da Daily Trust yayi da Dansadau ya ce sun yarda da cewa mayakan ISWAP ne kuma sun fara yada zango da farko a wani daji dake kusa da Shinkafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, sun kai wa Turji ziyara, shugaban hatsabiban ‘yan bindiga dake cin karensa babu babbaka a wuraren Shinkafi wurin watanni 3 da suka gabata.

Daga baya ‘yan bindigan suka ga sun takura a dajin sai suka canja sheka zuwa dajin Kuyambana dake masarautar Dansadau kuma suka cigaba da harkokinsu a can.
Mun yarda da cewa a cikin mayakan akwai ‘yan Najeriya da ‘yan kasashen ketare kuma suna kara mayar da dajin wuri mafi hatsari da ban tsoro saboda ko ‘yan bindiga suka ga wadannan shu’uman guduwa suke yi.
Abin ban tsoro ne saboda sun yada zangonsu a can, duk da dai suna yi wa ‘yan bindiga wa’azi akan su daina kai wa manoma da makwabtan dajin farmaki. Suna so ne su ja ra’ayin mazauna yankin don su so su saboda za su dawo da zaman lafiya yankin.

Kara karanta wannan

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

A wannan halin da ake ciki, duk wanda yayi alkawarin dawo da zaman lafiya a anguwanninmu zai soyu a idon jama’a. Tsoron da muke ji shine kada su koma su shirya wata tuggun a wurin.
Abin ban takaicin shine yadda mutanen suka iso a lokacin da sojoji suke tsaka da karar da ‘yan bindigan yankin. Ba a dade ba da sojoji suka kai wa ‘yan ta’adda hari a wata anguwa kusa da garin Charbi kuma sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama, a cewar Sanata Dansadau.

Sanata Dansadau ya mika kokon bara ga sojoji

Ya roki sojoji a kan dagewa da rike wuta akan duk wasu ‘yan bindiga. Ya ce su tabbatar sun rabu wuri-wuri har jihohin da suke makwabtaka dasu.

Yanzu da sojoji suke kai musu farmaki sai komawa dajin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna suke yi. Kuma muna da iyaka da jihar Katsina, idan sojoji za su yi aiki a Dansadau su hada har da Katsina don gudun ‘yan ta’addan su tsere can, kamar yadda ya bayar da shawara.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Sama da 40 a Jihar Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel