2023: Magoya bayan Saraki suna bin Jihohin Arewa, suna rabawa Manoma kayan gona

2023: Magoya bayan Saraki suna bin Jihohin Arewa, suna rabawa Manoma kayan gona

  • Saraki Is Coming Door To Door 2023 Organisation ta raba wa manoma taki
  • Kungiyar Magoya bayan Bukola Saraki ta yi rabon takin ne a jihohin Arewa
  • Shugaban wannan kungiya, ya yi kira ga Saraki ya fito takara a zaben 2023

Saraki Is Coming Door To Door 2023 Organisation ta raba taki

Wata kungiyar siyasa mai suna Saraki Is Coming Door To Door 2023 Organisation, ta yi rabon kayan gona ga manoma a wasu jihohin kasar nan.

Wannan kungiya ta Saraki Is Coming Door To Door 2023 Organisation ta na da burin ganin cewa Bukola Saraki ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kungiyar ta raba buhunan takin zamani ne ga manoma masu karamin karfi a duka jihohin Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu

Shugaban wannan tafiya na kasa, Umar Faringado-Kazaure, ya yi jawabi a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, yana bayyana dalilin yin hakan.

Da yake jawabi a garin Abuja, Malam Faringado-Kazaure yace wannan zai kara fito da alheran tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki.

Ina da ina aka raba wadannan kaya?

A cewar shugaban kungiyar Saraki Is Coming Door To Door 2023 Organisation, an yi rabon wadannan kaya a jihohi bakwai na Arewa maso yamma.

Kayan gona
Takin zamani 'dan Bukola Saraki Hoto: www.blueprint.ng
Asali: UGC

Jihohin da manoma suka amfana da buhunan takin zamanin sun hada da Kano, Katsina, Kaduna, da Jigawa, sai kuma Kebbi, Sokoto da kuma Zamfara.

“Muna yin wannan ne domin mu nuna wa Duniya wanene Dr. Abubakar Bukola Saraki. Mutum ne shi mai kaunar jama’a, ‘dan kishin kasa.”

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan

“Idan ya sake samun wata dama a gwamnatin tarayya, bangaren noma yana cikin abubuwan da zai ba karfi domin abinci ya wadata.”
“Kungiyarmu, ‘Saraki Is Coming Door To Door 2023’ ta raba taki ga kananan manoma domin cigaba da aikin alherin Bukola Saraki a kasar nan.”

A karshe, Umar Faringado-Kazaure ya yi kira ga tsohon gwamnan na Kwara da ya fito neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 domin ya ceci Najeriya.

Bukola Saraki zai yi takara a 2023?

A watan Yuli wata kungiya mai suna Sarakiyya 2023 ta bude ofisoshin yakin neman zabe mai zuwa na 2023 a jihar Katsina domin yi wa Bukola Saraki kamfe.

Abubakar Nuhu Adam Babban-Mutum shi ne shugaban kungiyar Sarakiyya da ta ke ganin tsohon shugaban majalisar dattawan ne ya dace ya rike Najeriya a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng