Magoya bayan Bukola Saraki suna kara karfi, sun shiga Katsina, sun fara yakin neman zaben 2023

Magoya bayan Bukola Saraki suna kara karfi, sun shiga Katsina, sun fara yakin neman zaben 2023

Sarakiyya 2023 ta na bude ofisoshin yi wa Bukola Saraki yakin zaben 2023

Abubakar Nuhu Adam Babban Mutum shi ne shugaban kungiyar Sarakiyya

Kungiyar ta na ganin tsohon shugaban majalisar ne ya dace ya rike Najeriya

Sarakiyya 2023 ta kai Jihar Shugaban kasa

Wata kungiya ta matasa a karkashin lemar Sarakiyya 2023 ta fara bude ofisoshin yakin neman zabe mai zuwa na 2023 a fadin jihar Katsina.

Jaridar Katsina Post ta ce kungiyar Sarakiyya 2023 ta kaddamar da ofisoshinta na jiha, shiyyoyi, da na kananan hukumomi a hedikwatar PDP.

Kungiyar Sarakiyya 2023 ta fito da wani samfurin hula mai launin kore da fari, a matsayin alamar gane magoya bayan Bukola Saraki a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya fara fada da mataimakinsa da ya zauna a PDP

Abin da ya sa mu ke yin Saraki - Abubakar Babban Mutum

Shugaban wannan kungiya, Honarabul Abubakar Nuhu Adam Babban Mutum, ya na yi wa Bukola Saraki shimfida ne domin ya yi takara a 2023.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya bayyana yayin da jama'a suka yi tururuwan fitowa don tarbar Shugaba Buhari a Kano

Abubakar Nuhu Adam wanda ake kira Babban Mutum ya na ganin tsohon gwamnan jihar Kwara, Saraki ne ya fi dace wa ya rike Najeriya a 2023.

Ganin irin rawar da Bukola Saraki ya taka a lokacin ya na shugaban majalisar dattawa, shiyasa Abubakar Nuhu Adam, ya ke goyon bayansa.

Bukola Saraki ya yi kokari wajen amince wa da kudirin Not Too Young To Run da ta ba matasa damar shiga takara, su samu kujerar gwamnati.

KU KARANTA: Gwamnan PDP ya caccaki Shugaban kasa Buhari

Sarakiyya 2023
'Yan Sarakiyya 2023 da korayen huluna Hoto: www.katsinapost.com.
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto Hon Abubakar Nuhu Adam ya na cewa Saraki ya yi namijin kokari domin ganin an samu matasa a majalisar koli ta jam’iyyar PDP.

“Mun yarda cewa za mu goya baya ga wanda wanda yake tare da matasa a zuciyarsa. Kuma a wurinmu, Saraki ne kawai ya fada wannan rukuni.”

Today ta ce magoya bayan sun yi kira ga PDP ta ba yankin Arewa maso tsakiya damar takarar shugaban kasa ta yadda gwarzonsu zai samu tikiti.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Idan mu ka koma siyasar Zamfara, za mu ji cewa jm’iyyar PDP ta dauko Lauyoyin da za su kare ta a shari’ar da za ta yi da wadanda su ka koma APC.

PDP ta kai karar Gwamna Bello Matawalle, ‘yan majalisar dokoki da na tarayya, jam’iyyar APC, shugabannin majalisa, da hukumar INEC gaban Kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel