Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan

  • Shugaban kasan Najeriya ya dawo gida daga kasar Birtaniya
  • A fitarsa da karshe a Landan, Buhari zai ziyarci abokin siyasarsa Bola Tinubu
  • Shugaban kasan ya halarci taron ilmi kuma ya ga Likitocinsa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gidan Najeriya bayan zaman ganin Likita na kimanin makonni biyu da yayi a birnin Landan, kasar Birtaniya.

Buhari ya dira a Abuja ne da yammacin Juma'a, 13 ga watan Agusta, 2021.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Femi Adesina, ya bayyana hakan da yammacin nan a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 26 ga Yuli, zai shilla kasar Birtaniya ganin Likitocinsa da kuma halartan taron ilimi na duniya kan hadin kai wajen zuba kudi fagen ilimi watau GPE 2021-2025.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Ahmad Joda, ya rasu

Bayan haka shugaba Buhari yayi zaman diflomasiyya da Firai Minista Boris Johnson.

Bayan taron, shugaban kasa zai kwashe yan kwanaki domin ganin Likitansa da ya kamata ace ya gani tun a baya. Zai dawo Najeriya a tsakiyar Agusta, 2021.

PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

Jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din.

PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.

PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng