Muhimman Abubuwa 9 Da Ya Dace a Sani Game Da Mayaƙan Taliban, Sabbin Shugabannin Afghanistan

Muhimman Abubuwa 9 Da Ya Dace a Sani Game Da Mayaƙan Taliban, Sabbin Shugabannin Afghanistan

  • Afghanistan ta zama filin yaki bayan mayakan Taliban sun kwace babban birnin Kabul a ranar Lahadi, 15 ga watan Augusta
  • Mayakan Taliban sun bayyana kasar a matsayin “daular musulunci” bayan shugaban kasa Ashraf Ghani ya tsere daga masarautar da kasar gaba daya
  • Hakan ya biyo bayan umarnin shugaban kasar Amurka, Joe Biden, na janye sojojin Amurka daga kasar a watan da ya gabata

Kabul, Afghanistan - Cikin kankanin lokaci Afghanistan ta zama filin daga tun bayan shugaban kasar, Ashraf Ghani ya tsere daga fadarsa da kasar bayan shugaban kasar Amurka ya janye sojojin kasarsa.

Muhimman abubuwa 9 da ya dace a sani game da mayakan Taliban
Muhimman abubuwa 9 da ya dace a sani game da mayakan Taliban. Hoto daga Javed Tanveer/AFP
Asali: Getty Images

A wannan labarin zakuji abubuwa 9 akan Taliban da mayakanta 85,000.

1. Shekaru 20 kenan bayan labaran Taliban sun karade duniya. Kusan duk wasu kananun yara a Najeriya basu da labarin kasar kasancewar shekaru 20 da ‘yan kai kenan da kasar ta samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Shugaban Afghanistan ya tsere da makudan kudade cike da jirgi da motoci

Cikin kwanakin nan labaran Taliban sun fara zagaye duniya bayan kwace Kabul, babban birnin Afghanistan da mayakan suka yi cikin kankanin lokaci.

Mayakan Taliban sun yi zobe a kofar shiga ma’aikatar cikin gida dake Kabul a ranar Talata, 17 ga watan Augusta.

A shekarar 1994 ne kowa yaji labarin Taliban, lokacin yakin farar hula wanda mafi yawancin mayakan dalibai ne.

2. Taliban din da Mullah Mohammed Omar yake shugabanta ta fara mallakar Herat ne kafin ta kwace gaba daya kasar a watan Satumbar 1996, inda suka kori Burhanuddin Rabbani daga shugabanci kuma suka kafa daular musulinci a Afghanistan.

3. Duk da dai ta diflomasiyya ne Pakistan ta amince da sabuwar daular, mazauna kasar sun san Taliban tuntuni.

4. Sun wajabta bin shari’ar musulunci kuma dole a bi doka da karfi da yaji, sun dakatar da amsar abinci da majalisar dinkin duniya wacce take tallafa wa talakawa da masu kananun karfi suke samarwa. Dole ne shiga irin ta musulunci a kasar kuma sun hana yara mata aiki, tafiya da kuma karatu.

Kara karanta wannan

Dakarun Amurka sun gana da shugabannin Taliban kan batun Amurkawa

5. Sun dakatar da fim da duk wasu abubuwan da addinin musulunci ya hana sannan suna rusa duk wasu gumaka a fadin kasar.

6. A watan Disamban 2001 ne Amurka ta hada karfi da karfe wurin dakatar da mulkin Taliban, hakan ya janyo tashin hankali a birnin New York wanda sai da mutane 2,996 suka rasa rayukansu sannan mutane 25,000 suka samu miyagun raunuka.

7. Daga nan shugaban Al-Qaeda, Osama bin Laden wanda daya ne daga cikin shugabannin Taliban na Afghanistan ya shirya kai wani farmaki.

8. Duk da sun sha kasa, mayakan Taliban sun kara taruwa sun cigaba da kai hari Amurka.

9. Yanzu haka Mawlawi Haibatullah Akhundzada ne shugaban Taliban, ya gaji Mullah Akhtar Mohammed Mansour a shekarar 2016 bayan Amurka ta kai hari Pakistan wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa. Yanzu haka yana jagorantar mayaka 85,000.

An sake kashe mutum 5 a wani hari a Jihar Plateau

A wani labari na daban, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mutane biyar a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau kamar yadda News Wire NGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Komai ya dawo daidai: Shugaba Buhari zai fito daga kullen Korona ranar Laraba mai zuwa

An gano cewa an kashe mutanen biyar ne a yayin da yan bindigan suka kai hari kauyen Chando-Zrrechi (Tafi-Gana) a daren ranar Talata.

News Wire NGR ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Cigaban Irigwe na kasa, Ezekiel Bini, ya tabbatar da kisan a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel