Shugaban Afghanistan ya tsere da makudan kudade cike da jirgi da motoci

Shugaban Afghanistan ya tsere da makudan kudade cike da jirgi da motoci

  • Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar Afghanistan ya tsere da wasu makudan kudade
  • An ce, an ga motoci hudu da kuma jirgi makare da kudade lokacin da shugaban yake tserewa
  • Rasha ce bayyana wadannan bayanai ga jaridar Reuters da kuma sauran manema labarai

Afghanistan - Ofishin jakadancin Rasha da ke Kabul ya fada a ranar Litinin 16 ga watan Agusta cewa, shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya tsere daga kasar da motoci hudu da jirgi mai saukar ungulu cike da tsabar kudi har suna zuba.

Ghani, an ce ya bar Afghanistan ranar Lahadi yayin da Taliban ta shiga Kabul, wanda a cewarsa yana son kaucewa zubar da jini, a cewar Independent.

Shugaban Afghanistan ya tsere da makudan kudade cike da jirgi da motoci
Ghani Ashraf | Hoto: aljaseera.com
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labaran RIA ya nakalto Nikita Ishchenko, mai magana da yawun ofishin jakadancin Rasha a Kabul yana cewa:

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

"Dangane da rugujewar tsarin mulki (mai barin gado), ya shahara da yadda Ghani ya tsere daga Afghanistan."
"Motoci hudu cike suke da kudi, sun yi kokarin cusa wani sashi na kudin a cikin jirgi mai saukar ungulu, amma ba duka ne suka shiga ba. Kuma an bar wasu daga cikin kudin a zube akan kwalta."

Ischenko, kakakin ofishin jakadancin Rasha, ya tabbatar da wadannan kalaman nasa ga kamfanin dillacin labarai na Reuters. Ya kawo “shaidu” a matsayin tushen bayanansa, duk da cewa jaridar ba ta iya tantance sahihancin bayanan ba.

Wane adadi gwamnati mai tserewa ta bari a kasar?

Wakilin shugaba Vladimir Putin na musamman kan Afghanistan Zamir Kabulov ya ce tun farko ba a san adadin kudin da gwamnatin da ke tserewa za ta bari ba.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Kabulov ya fadawa gidan rediyon Ekho Moskvy na Moscow cewa:

"Ina fatan gwamnatin da ta gudu ba ta kwashe dukkan kudade daga kasafin kudin kasar ba. Zai zama ginshikin kasafin kudin idan aka bar wani abu."

A bangare guda, Rasha ta ce za ta ci gaba da kasancewar diflomasiyya a Kabul kuma tana fatan ci gaba da kulla alaka da Taliban duk da cewa ta ce ba za ta gaggauta wajen yarda da su a matsayin masu mulkin kasar ba, kuma za ta lura da halayen su sosai.

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

A wani labarin, Kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta sanar da yin afuwa a fadin kasar tare da kira ga mata da su shigo cikin sabuwar gwamnatinta, Aminiya ta ruwaito.

Taliban ta yi hakan ne a kokarinta na kwantar da hankula a Kabul, babban birnin kasar, inda mutane suka yi ta turmitsutsi a filin jirgin sama domin ficewa daga kasar bayan kungiyar ta hambarar da gwamnatin kasar da Amurka ke marawa baya.

Kara karanta wannan

Komai ya dawo daidai: Shugaba Buhari zai fito daga kullen Korona ranar Laraba mai zuwa

Cikin wata sanarwar dauke hannun Enullah Samangani daga hukumar raya al'adu ta Taliban, wacce ita ce ta farko da Taliban ta fitar tun bayan hambarar mulkin shugaba Ashraf Ghani, ta ce:

“Masarutar Musulunci ta (Afghanistan) ba ta so a kuntata wa mata, muna kira da su shigo gwamnati bisa tsarin Musulunci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel