Dakarun Amurka sun gana da shugabannin Taliban kan batun Amurkawa

Dakarun Amurka sun gana da shugabannin Taliban kan batun Amurkawa

  • A can kasar Afghanistan, sojojin Amurka sun gana da shugabannin Taliban don fayyac wani batu
  • Batu ne kan yadda kasar Amurka za ta tattara dakarunta da kuma Amurkawan da ke cikin kasar
  • Har yanzu dai Taliban na ci gaba da cewa, ita ba abinda ke gaban ta illa wanzar da zaman lafiya a kasar

Afghanistan - Amurka ta bayyana cewa dakarunta sun gana da shugabannin Taliban da suka kwace mulki a kasar Afghanistan, in ji Aminiya.

Kakakin Sakataren Tsaron Amurka, John Kirby, ya ce kwamandojin kasar da ke filin jirgin sama na Kabul, babban birnin Afghanistan na ganawa da Taliban “a matakin Afghanistan, muna kuma tattaunawa da su kan kwaso Amurkawa”.

The Columbian ta ruwaito cewa, Kirby shaida wa ’yan jarida a Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) cewa:

Kara karanta wannan

Taliban: Ba ma gaba da kowa, mun yafe wa duk wadanda suka yake mu a baya

Dakarun Amurka sun gana da shugabannin Taliban kan batun Afghanistan
Shugabannin Taliban | Hoto: guardian.co.uk
Asali: Getty Images

“Nan gaba ne za a san me zai faru, amma tabbas kwamandojinmu suna magana da shugabannin Taliban domin kammala aikin da suka je yi a can."

Hakazalika, Janar Frank McKenzie, shugaban rundunar Amurka, ya gargadi jami'an Taliban cewa sojojin Amurka za su mayar da martani da karfi don kare filin jirgin sama idan hakan ya kama.

Taliban: Ba ma gaba da kowa, mun yafe wa duk wadanda suka yake mu a baya

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar kowanne dan kasar Afghanistan ya samu damar walwala tana mai cewa ba ta bukatar abokan gaba.

A taron manema labarai da ta gudanar, mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid, wanda ya bayyana a gaban 'yan jarida a karon farko tun bayan da suka kwace iko, ya ce sun 'yantar da kasar.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

A cewarsa in ji rahoton BBC:

"Bayan shekaru 20 na fafutuka kuma mun kori 'yan kasashen waje."
"Wannan lokaci ne na alfahari."
"Muna son tabbatar da ganin Afghanistan ba ta sake tsunduma cikin yaki ba. Mun yafe wa dukkan mutanen da suka yake mu. Gaba ta zo karshe."

Afghanistan: Sabanin abinda ake tsoro, Taliban za ta dama da mata a mulkinta

A wani labarin, Kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta sanar da yin afuwa a fadin kasar tare da kira ga mata da su shigo cikin sabuwar gwamnatinta, Aminiya ta ruwaito.

Taliban ta yi hakan ne a kokarinta na kwantar da hankula a Kabul, babban birnin kasar, inda mutane suka yi ta turmitsutsi a filin jirgin sama domin ficewa daga kasar bayan kungiyar ta hambarar da gwamnatin kasar da Amurka ke marawa baya.

Cikin wata sanarwar dauke hannun Enullah Samangani daga hukumar raya al'adu ta Taliban, wacce ita ce ta farko da Taliban ta fitar tun bayan hambarar mulkin shugaba Ashraf Ghani, ta ce:

Kara karanta wannan

Buhari ga turawan yamma: Ba ma bukatar sojojinku, hannun jari muke bukata

“Masarutar Musulunci ta (Afghanistan) ba ta so a kuntata wa mata, muna kira da su shigo gwamnati bisa tsarin Musulunci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel