Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m

Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m

  • Gift Agenoisa, wata dalibar JSS1 a makarantar sakandaren Mary Immaculate dake Ado-Ekiti, ta maka gwamnatin jihar Ekiti a babbar kotun jihar
  • Gift tana bukatar gwamnati ta biya ta naira miliyan 15 sakamakon shiga hakkinta da gwamnatin tayi na dakatar da karatunta a makaranta
  • Dalibar ta je makaranta da wani kitso ne wanda ya keta dokar makarantar, ta fuskanci horo mai tsanani a makarantar, lamarin da yasa taje kotu

Ado-Ekiti, Ekiti - Gift Agenoisa, dalibar JSS1 a makarantar sakandare ta Mary Immaculate dake Ado-Ekiti ta maka gwamnatin jihar Ekiti a gaban babbar kotun jihar tana bukatar gwamnatin ta biyata naira miliyan 15 sakamakon shiga hakkinta na ‘yar adam.

Korafin nata mai lamba HAD/01/CR/2021 wanda Odunayo Agenoisa ya gabatar ga babbar kotun Ado-Ekiti a maimakonta, wanda dalibar tayi ikirarin dakatar da karatunta da gwamnatin tayi ya shiga hakkinta na bil’adama.

Kara karanta wannan

Kaduna: Majalisar jiha ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta

Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m
Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a takardar ta bayyana irin cutarwa da zaluncin da aka mata, akan zuwanta makaranta da wani kitso wanda suke ganin bai dace ba.

Su waye dalibar ta kai kara?

A cikin korafinta ta sanya Shugaban makarantar, Mrs Oluwasanmi F.M, kwamishinan ilimin jihar, Dr Olabimpe Aderiye, shugaban malaman jihar da kuma gwamnatin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A takardar kotun data hada ta bayyana yadda aka kira ta gaban gaba daya daliban makarantar a ranar 22 ga watan Mayu sannan aka yi mata bulalai 20 bisa umarnin shugaban makarantar.

A asalin takardar da lauyanta, Mr Timmy Omotoso ya gabatar, ya kawo dokoki kwarara na 1,3,4,5 da 6 na hakkin bil’adama na 2009 wadanda sashi na 315 suka gabatar daga kundin tsarin mulkin 1999, ta bukaci naira miliyan 15 akan dakatar da karatunta da sukayi.

Kara karanta wannan

FG na bibiyar Kanu da Igboho amma ta kyale barayin makiyaya, Gwamnan Arewa

Ta bukaci a yi gaggawar mayar da ita makaranta don ta cigaba da karatunta.

Wanne mummunan hali dalibar ta shiga bayan dukan?

Yarinyar ta bayyana yadda ranar da ta sha dukan ta samu miyagun raunuka wadanda sai dai ta tafi kabarinta da tabo, jini yayi kaca-kaca da suturarta sannan ta suma take a wurin kafin aka wuce da ita asibitin ‘yan sanda dake Ado-Ekiti, inda aka duba lafiyarta.

Ta kara bayyana yadda wasikarta ta korafi wacce ta tura wa matar gwamna da sauran masu fadi a ji a jihar ta tashi a tutar babu.

Tace yanzu haka an hana ta zuwa ko harabar makarantar bisa umarnin shugaban makarantar tun a lokacin.

A ranar 22 ga watan mayu, mahaifin yarinyar da wani dan sanda, Elijah, suka gayyaci wasu ‘yan sanda hudu suka ci mutuncin wasu malaman makarantar akan abinda aka yi wa diyarsa akan kitson da suka ce bai dace da tsarin makarantar ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel