Kaduna: Majalisar jiha ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta

Kaduna: Majalisar jiha ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta

  • Majalisar jihar Kaduna ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta, Mukhtar Isa-Hazo
  • Kamar yadda kakakin majalisar ya bada umarni magatarkadan majalisa ya aikewa Hazo sakon ya dawo bakin aikinsa
  • A zaman majalisar da aka yi, wani dan majalisa ya roka a madadin Hazo wanda yace yana ta neman yafiyar majalisar

Kaduna - Majalisar jihar Kaduna ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta, Mukhtar Isa-Hazo, dan majalisa mai wakiltar mazabar Basawa.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, an dakatar da Hazo tare da wasu 'yan majalisa uku fiye da shekara daya da ta gabata.

Kaduna: Majalisar jiha ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta
Kaduna: Majalisar jiha ta dage dakatarwar da tayi wa tsohon mataimakin kakakinta. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Waye ya mika bukatar gaban majalisar?

Hukuncin ya biyo bayan wata bukata da Ahmad Muhammad, dan majalisa mai wakiltar mazabar Zaria da Kewaye ya mika yayin zaman majalisar a ranar Laraba a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammad ya ce:

Ina tsaye a yau a gabanku domin tunatar daku cewa a watan Afirilun shekarar da ta gabata, na kawo bukatar dakatar da wasu 'yan majalisa hudu.
Sunansu, Alhaji Mukhtar Isa Hazo, tsohon mataimakin kakakin majalisa, Salisu Isa, mai wakiltar mazabar Magajin Gari, Alhaji Yusuf Liman, mai wakiltar Makera/Kakuri da Nuhu Goro Shadalafiya mai wakiltar mazabar Kagarko.
A don haka yau nake rokon kakakin majalisa da sauran 'yan majalisa a madadin Alhaji Mukhtar Isa-Hazo mai wakiltar mazabar Basawa, wanda ya dinga roko a bainar jama'a ba sau daya ko biyu ba.
Sakamakon nadamar da ya nuna, ina rokon kakakin majalisa da ya duba lamarin tare da kira su su dawo aikinsu na majalisa."

Kamar yadda yace, hakan zai zama izinina ga sauran 'yan majalisar uku da su fito a fili su nuna nadamarsu domin a kira su su dawo bakin aikinsu.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta magantu kan karrama Abba Kyari da ta yi a matsayin gwarzo

Fatanmu ne cewa zasu dawo tare da mu a zaman majalisa na gaba, Muhammad ya roka.

Me kakakin majalisa yace a kai?

A jawabinsa, kakakin majalisa Yusuf Zailani, ya ce ba zai taba kin karbar wannan bukata ba kuma yana jiran sauran 'yan majalisan uku da su nemi gafara.

Ya umarci Magatakardan majalisa da ya bayyana wannan hukunci ga Isa-Hazo domin ya dawo aikinsa, Channels TV ta ruwaito.

Ubangijin da muke bautawa mai yafiya ne, kuma idan ka cutar da wani ka yafe masa, Ubangiji zai yafe maka naka zunubban.
Yau ranar farin ciki ce gareni ta yadda daya daga cikin abokaina ya mika bukatar kiran sauran abokaina su dawo aikinsu. Komai da zai faru, Hazo abokina ne kuma zamu cigaba da abokantaka, kakakin majalisa yace.

A ranar 11 ga watan Augustan 2020, an dakatar da 'yan majalisa hudu sakamakon tada tarzoma yayin zaman majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: