Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

  • Wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan labarai na jihar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun sake shi ranar Lahadi da dare
  • Sai dai abin al’ajabi shine ko sisi ba a biya ba sai gashi sun sako kwamishinan kamar yadda ya tabbatar
  • Bayan sakin shi ne kwamishinan yace da gwamnati ta kuskura ta biya sisi don a sake shi da ya yi murabus bayan fitowarsa

Minna, Niger - Kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Muhammed Sani Idris, wanda ya samu 'yanci daga hannun 'yan bindiga a daren ranar Alhamis, da ace gwamnati ta biya kudin fansa domin karbarsa, toh babu shakka murabus zai yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Idris ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labari a Minna, babban birnin jihar inda ya karba bakuncin kakakin majalisar jihar, Rt Honarabul Abdullahi B Wuse da sauran 'yan majalisar.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Neja da aka sako ya bayyana wadanda suka sace shi

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger
Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger. Hoto dailytrust.com
Asali: UGC

Wanne kalubale kwamishinan ya fuskanta a hannun miyagu?

Ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta lokacin da yake hannun masu garkuwa da mutane.

A cewarsa duk da azaba da cutarwar da ya fuskanta a hannunsu, ya jajirce kuma ya dage.

Hakika al’amarin akwai razanarwa. Da na fita jiya da daddare, na je asibiti don a kara duba jikina kuma komai lafiya lau.
Ni kadai suka sata don sun ganni a babban mutum ne don haka sai da suka dage kwarai don su tabbatar sun samu nasara. Ba cetona aka yi ba kuma ko sisi ban biya ba. Abin gwanin ban al’ajabi.
Da farko sun fara takura ni suna cutar dani iyakar cutarwa irin wacce ba kowanne dan’ Adam ne zai iya jurewa ba; sai dai ubangiji ya taimakeni, saboda na kasance cikin imani.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi

Na tambayesu idan abinda suke yi daidai ne a wurin Allah, maimakon su rusa ni, sai na fara rusasu.
Bayan nan ne suka fara bani biredi da ruwa. Sun kwance ni sai suka fara amfani da tamfal suna lullubeni idan ana ruwan sama.
Sai suka fara nuna damuwa a kaina, ni kuma na cigaba da yi musu wa’azi, sai suka ce in koma wurin iyalina in gansu,” a cewarsa.

Kwamishina ya yabawa gwamnati da bata biya kudin fansa ba

Kwamishinan ya yabawa gwamnan jiharsa akan tsayawa tsayin-daka wurin kin biyan ko sisi ga wadanda suka yi garkuwa dashi, inda yace yana alfahari da jihar Neja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Abin farko da na fara yi bayan sun sakeni shine in tura sakona ga gwamna akan jajircewarsa da kwarin guiwa akan yadda gwamnatin jihar Neja taki amincewa da biyan kudi ga masu garkuwa da mutane kamar yadda hakan ta faru dani.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamnatin Buhari ta ware wa 'yan sanda kudin sayen man fetur

Sun zo da muryoyi da suka dauka a waya inda nake tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar Neja bata biyan masu garkuwa da mutane ko sisi.
Na tabbatar zamu cigaba. Nagode wa gwamnatin jihata akan tsayawa tsayin-daka wurin kare martabarmu.
Lokacin da nake hannun masu garkuwa da mutane duk tunanina yana kan mutanenmu da gwamnatin jihar Neja saboda nasan idan Ubangiji bai kawo dauki ba akwai babbar matsala.
Na gwammaci in rasa raina akan a ciri sisi a biya su. Na fito tsaf ba tare da an biya ko sisi ba kuma babu ko alamar duka a jikina.
Mutane da dama zasu yi mamaki amma kuma ni mai imani ne don haka ba abin mamaki bane. Lokacin da suka saceni na tuna da cewa Ubangiji ya yi alkawarin taimakawa duk wanda yayi imani dashi,” a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel