Darajar Naira ya kuma sauka kasa, farashin Dalar Amurka $1 ya dumfari N515 a kasuwa

Darajar Naira ya kuma sauka kasa, farashin Dalar Amurka $1 ya dumfari N515 a kasuwa

  • Naira ta cigaba da rasa kima a kasuwar canji, ita kuma Dala ta na kara tashi
  • Farashin Dalar Amurka ya kara daraja a makon nan daga N510 zuwa N515
  • A karshen watan da ya wuce CBN ta daina alaka da ‘Yan Bureaux de Change

Najeriya - A ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, 2021, kudin Najeriya na Naira ya rasa kimar da ya samu a kan Dalar Amurka a cikin ‘yan kwanakin nan.

Nawa ne farashin Dala a yau?

Jaridar Punch ta ce yayin da ake fama da karancin kudin kasar waje a halin yanzu, darajar Naira ya ragu a kasuwar canji a cikin tsakiyar wannan makon.

Farashin Dalar Amurka ya kai N515, hakan ya na nufin Naira ya rasa N5 a cikin sa’a 24. Kafin Laraba, an saida kowane Dalar Amurka ne a kan N510.

Kara karanta wannan

Kungiyar Barcelona za ta gamu da rashin kudi na inna-naha bayan tashin Lionel Messi

Rahoton ya ce Nairar ta yi hobbasa ne a ranar 4 ga watan Agusta, lokacin da Dalar Amurka ta koma N506, kafin nan sai da aka saida Dala a kan N525.

Tun bayan lokacin da ‘yan canji na Bureaux de Change suka daina samun kudi daga CBN, farashin Dalar yake ta yawo tsakanin N508 zuwa N510.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Naira ta kara karfi a wajenmu - FMDQ

FMDQ Group ta bayyana cewa Naira ta na kara daraja ne a wajenta, kudin gidan ya kara kima da 0.02% a hannun masu alaka da masu kasuwanci a ketare.

Bankin CBN
Babban bankin kasa na CBN Hoto: technext.ng
Asali: UGC

Rahoton ya nuna cewa masu karbar Dala da sauran kudin kasar waje domin su shigo da kaya daga ketare sun saye kowane Dalar Amurka a jiya a kan N411.

Alkuma sun tabbatar mana an samu raguwar masu fita fatauci a kasashen ketare a makon nan, abin da aka kashe ya ragu daga $590m zuwa $489m a jiya.

Kara karanta wannan

Ranar kin dillaci: EFCC ta karbe manyan gidaje, motoci da miliyoyi a hannun wasu ‘Yan damfara 2

Matakin da CBN ta dauka

Naira ta yi raga-raga ne bayan matakin da babban bankin kasa na CBN, ya dauka a karshen watan Yuli, na hana saida wa ‘yan canji kudin kasashen waje.

Godwin Emefiele ya bada sanarwar hana masu kasuwancin BDC kudin ketare, saboda ana hada-kai da su wajen yin ta’adi, aka koma ba bankuna kasonsu.

Najeriya na fuskantar matsalar cin bashi

An ji cewa Indiya da Najeriya suna cikin kasashen da su ka fi kowane yawon cin bashin kudi a Duniya. An fara tsoro kar bashi ya yi wa kasashen nan katutu.

Sai dai duk da haka, gwamnatin Najeriya ba ta yarda cewa yawan bashi zai yi mata daurin goro ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel