Bashin biliyoyin dalolin kudin da ake bin Najeriya da wasu kasashe 9 ya yi yawa inji Bankin Duniya

Bashin biliyoyin dalolin kudin da ake bin Najeriya da wasu kasashe 9 ya yi yawa inji Bankin Duniya

  • Bincike ya nuna Najeriya na cikin sahun kasashen da su ke da yawan cin bashi
  • Bankin Duniya ya na ganin neman aron kudin na iya jefa kasashe 10 a matsala
  • IDP ta ce Najeriya, Indiya, Kenya da Uganda sun shiga jerin wadannan kasashe

A ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, 2021, Punch ta rahoto cewa Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin kasashe goma da suke fuskantar matsalar bashi.

Babban bankin Duniyan ya bayyana hakan ne a rahoton da kungiyar International Development Association ta fitar na wannan shekarar a farkon makon nan.

Rahoton kudin yace akwai wasu kasashen Duniya da ba za su iya cika yarjejeniyar da suka dauka ba.

Su wanene kasashe goma da su ka yi kaurin suna?

Jaridar ta ce sakamakon binciken da aka yi ya nuna cewa zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2021, akwai kasashe goma da suka fi kowane shiga cikin matsin.

Kara karanta wannan

Bincike: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura saboda wasu dalilai

A sahun wadannan kasashen, Najeriya mai Dala biliyan 11.7 ce ta zo ta biyar, yayin da kasar Indiya ce ta zo ta farko da bashin fam dala biliyan 22 a kanta.

Sauran kasashen da suka shiga wannan sahu sun hada da Habasha, Kenya, Tanzaniya, Ghana da Uganda. Duka wadannan kasashe suna cikin nahiyar Afrika.

Economic Advisory Council
Buhari da Majalisar Economic Advisory Council Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Kungiyar International Development Association ta tsaida bashin da ke kan wadannan kasashe biyar kan; $11.2bn, $10.2bn, $8.3bn, $5.6bn, sai kuma $4.4bn.

Halin da Najeriya ta ke ciki

Zuwa watan Yunin da ya wuce, abin da ya kamata Najeriya ta biya babban bankin na Duniya ya kai fam dala biliyan $8.656 (sama da Naira biliyan 100 kenan).

Punch ta ce an ci ma yarjejeniyar bashin Dala biliyan daya tsakanin Najeriya da bankin Duniyan, daga ciki abin da ya rage a gama biya shi ne fam miliyan $411.

Alkaluman ofishin bashi na kasa watau DMO, sun tabbatar da cewa zuwa karshen Mayun 2021, Najeriya ta karbi aron Dala biliyan 11.51 daga bankin Duniya

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Shugaban bankin Duniya, David Malpass, ya ce sun raba wa kasashe akalla dala biliyan 157 daga shekarar bara zuwa yanzu da nufin ayi yaki da cutar COVID-19.

Babu matsala - Gwamnatin Buhari

A yayin da ake korafe-korafe game da nauyin bashin da ke kan Najeriya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta na cewa larurori suke tilasta mata karbo aron kudi daga waje.

Bashin kudin da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 28.63. Duk da haka, gwamnati ta ce ba za ta daina aron kudin da za a yi wa 'yan kasa ayyukan more rayuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel