Kungiyar Barcelona za ta gamu da rashin kudi na inna-naha bayan tashin Lionel Messi

Kungiyar Barcelona za ta gamu da rashin kudi na inna-naha bayan tashin Lionel Messi

  • Tashin Lionel Messi zai sa Barcelona ta rage samun wasu kudin shiga
  • Daraja da sunar da kungiyar kwallon kafan zai fara yin kasa a yanzu
  • Biliyoyin kudin da Barcelona ta ke samu daga saida rigunanta zai ragu

Barcelona - A dalilin tashin Lionel Messi daga Barcelona, kulob din za ta gamu da asara a cikin filin wasan kwallon kafa da kuma wajen filin kwallo.

Za a yi rashin Messi a fili da wajen fili

Jaridar Marca ta ce tashin tauraron zai bar wa Ronald Koeman gibin da watakila ba zai yiwu a cike ba.

Bugu da kari, kungiyar kwallon kafar ta Sifen za ta yi asarar kudi masu yawa a asusunta, duk da ta huta da biyan tulin albashin tauraron ‘dan kwallon.

Ko da Messi ya na karbar albashin da babu wanda yake samu a Duniya a kungiyar ta shiyyar Catalan, ya na jawo wa Barcelona makukun kudin shiga.

Kara karanta wannan

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

Darajar Barcelona za ta yi kasa a 2021

Marca tace wani rahoto da Brand Finance ta fitar, ya bayyana cewa tashin Lionel Messi zai sa darajar sunan Barcelona ya sauka kasa da kashi 11%.

Hakan ya na nufin kungiyar za ta iya asarar fiye da fam miliyan €137. Abin da wannan yake nufi shi ne a kudinmu na Najeriya, za ayi asarar N56.44bn.

Camp Nou
Filin wasan Camp Nou Hoto: @Barcelona
Asali: Getty Images

A shekarar da ake ciki ta 2021, Barcelona ta na cikin kungiyoyin kwallon kafan da su ka fi daraja a Duniya, ta zo bayan Real Madrid wanda ita ce a farko.

Gaza ajiye Lionel Messi a Barcelona zai sa kungiyar ta rasa wasu kudin da ta ke samu wajen kasuwanci kamar ta harkar tallar riguna a duk shekara.

A kowace shekara, Barcelona na iya rasa fam miliyan €77 saboda ta daina buga rigunan Messi. Ana maganar sama da Naira biliyan 30 ne a shekara.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Barcelona sun kai kara da nufin haramtawa PSG daukar Lionel Messi

Haka aka yi da Ronaldo ya bar Madrid

Real Madrid ta gamu da wannan kalubale a lokacin da tauraron ‘dan wasan nan na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bar kungiyar a kakar 2018.

Ana lissafin cewa darajar Real Madrid ya yi kasa da 19% bayan Cristiano Ronaldo ya koma Juventus.

Ana tsakiyar buga Gasar cin kofin Duniya na 2018, sai aka ji ‘Dan wasan Duniyan zai bar Real Madrid bayan ya shafe kusan shekaru 10 ya na wasa a Sifen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel