Ranar kin dillaci: EFCC ta karbe manyan gidaje, motoci da miliyoyi a hannun wasu ‘Yan damfara 2
- Jiya hukumar EFCC ta ci galaba a kan wasu matasa da ke damfarar al’umma
- Lauyoyin EFCC sun sa Alkali ya karbe kadarorin da ‘Yan damfara suka tara
- An raba ‘yan damfarar da motocin N30m da gidaje na fiye da N200m a Legas
Lagos - EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa ta ci nasara a kan wasu ‘yan damfara biyu; Tobilola Ibrahim Bakare da Alimi Seun Sikiru.
Kamar yadda Legit.ng ta samu labari, hukumar EFCC ta karbe dukiya mai yawa a hannun wadannan masu damfarar Bayin Allah bayan da aka shiga kotu.
EFCC ta fitar da bayani a shafin Facebook a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021, ta ce ta raba ‘yan damfarar da kadarorinsu bayan sun gaza kare kansu a kotu.
Wadannan mutane sun gaza gamsar da kotu cewa su ne suka mallaki dukiyoyin da aka samu a hannunsu.
Dukiyoyin da kotu ta damka wa Gwamnati
Hukumar ta EFCC ta ce dukiyoyin da za a damka wa gwamnatin tarayya su ne:
- Manyan gidaje uku a Lekki, jihar Legas
- Sama da Naira miliyan 200 a asusun banki
- Motoci masu tsada.
A asusun bankin wadannan mutane, an samu N196, 741, 216.82 da N7, 054, 852.0. An kuma karbe motoci biyu; Mercedes Benz E500 da wata Toyota Hilux 2020.
Katafaren gida mai dakuna biyar a layin Ibrahim Eleto Street, Osopa London, Lekki da kuma wani gida mai dakuna hudu a Ologolo , Jakande, Lekki, Legas.
Haka zalika an karbe wani gida mai dakuna hudu da ke kan titin Chevron Alternative, duk a Lekki.
Kamar yadda EFCC ta bayyana, babban kotun na Legas ya yi wa motocin kudi a kan Naira miliyan 30, sannan gidajen uku sun tashi a kan Naira miliyan 230.
Tobilola Ibrahim Bakare mai shekara 27 mutumin garin Ijebu Ode ne a jihar Ogun ya na karyar ‘dan kasuwa ne shi, alhali ya na satar dukiyar mutane ne.
Alkali O. A Taiwo ya zartar da hukuncin daurin shekaru uku a kan Bakare da Sikiru, za su iya karbar kansu da tarar Naira miliyan uku da Naira miliyan daya.
An yi irin haka a jihar Imo
Dazu kun samu rahoto wani Alkalin babbban kotu da ke Imo ya karbe kadarori da suka hada da Otel da jami’ar da Rochas Okorocha da Iyalinsa suka mallaka.
Alkali ya damkawa Gwamnati Hope Uzodinma wadannan kadarori bayan lauyan da ya tsaya wa Sanata Okorocha a gaban kotu ya gaza wanke shi daga zargi.
Asali: Legit.ng