Biliyoyin kudin VAT da Gwamnatin Buhari ta ke samu duk wata zai koma aljihun Gwamnoni

Biliyoyin kudin VAT da Gwamnatin Buhari ta ke samu duk wata zai koma aljihun Gwamnoni

  • Rahotanni sun nuna kudin shigan da gwamnatin tarayya ke samu zai ragu
  • Alkali ya ba gwamnatin jihar Ribas gaskiya a shari’ar ta da FIRS a kan VAT
  • Gwamnatin Tarayya ta samu N2.5tr daga VAT bayan an kara harajin a 2020

Abuja - Bisa dukkan alamu, gwamnatin tarayya za ta rasa makudan kudin da ta ke samu daga harajin VAT, game da karancin kudin shiga da ake fuskanta.

Daily Trust ta ce gwamnatin tarayya ta gamu da karin cikas a lokacin da ake kuka da tasgaron da annobar cutar COVID-19 ta kawo wajen samun kudin shiga.

Ya gwamnatin tarayya ta kare a kotu?

Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da kotu ta yi, inda aka ba gwamnatin jihar Ribas gaskiya a karar da ta kai game da wanda ke da alhakin karbar VAT a jiha.

Lauyan gwamnatin Ribas, Donald Chika Denwigwe (SAN), ya nemi kotu ta raba gardama ko tsakanin gwamnoni da FIRS a kan inda harajin VAT zai shiga.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari zata koma amsan kudin 'Toll Gate' hannun mutane

Lauyan da ya tsaya wa hukumar FIRS, O.C. Eyibo, ya fara nuna gwamnati za ta daukaka kara.

Jaridar ta ce mafi yawan kudin da gwamnatin tarayya ta ke samu ya na fito wa ne daga arzikin mai, yayin da gwamnoni ke raina kason da ake ba su duk wata.

Gwamnatin Buhari
Buhari ya kara VAT Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A daidai lokacin da wannan hukunci zai taimaki jihohin da za su iya karbe harajin VAT na kayan masarufi sosai, wasu jihohin sun dogara ne da gwamnatin sama.

BudgIT ta ce a cikin jihohi 36 da birnin tarayya, jihohi biyar ne suka fi bada gudumuwa a asusun VAT. Legas,, Ogun da Ribas da ta kai gwamnati kotu suna cikinsu.

Naira Tiriliyan 2.5 a shekara daya da rabi

Rahoton yace bayan Muhammadu Buhari ya kara VAT zuwa 7.5% a shekarar bara, Najeriya ta samu Naira tiriliyan 2.5 tsakanin Junairun 2020 da Yunin 2021.

Alkaluman da NBS ta fitar sun nuna cewa a rabin shekara, gwamnatin tarayya ta samu fiye da Naira tiriliyan daya a 2021, wannan labari ya na daf da ya canza.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri kan tafiya kasar waje

Bola Tinubu ya na tatsar kudin jihar Legas

A jiya ne kuma aka ji cewa Bode George ya soki aniyar Bola Tinubu na zama shugaban kasa, ya ce duk masu goyon bayan Tinubu a 2023 ba kalau kansu ya ke ba.

A cewar jigon na PDP, har gobe Bola Tinubu ya na amfani da kamfaninsa, yana tatsar arzikin jihar jihar Legas duk wata, da sunan gwamnati ta na karbar haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel