Gwamnatin Buhari zata koma amsan kudin 'Toll Gate' hannun mutane

Gwamnatin Buhari zata koma amsan kudin 'Toll Gate' hannun mutane

  • Bayan shekaru aru-aru, za'a koma amsan kudi kan manyan tituna
  • Ministan ayyuka ya dade da bayyana niyyarsa kuma yanzu gwamnati ta amince
  • Masu motocin haya da na zaman kansu zasu biya N200 zuwa N300

Gwamnatin tarayya ta amince da dawo da tsarin biyan kudin 'Toll Gate' na karban kudin hannun motoci a manyan titunan Najeriya, hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, ya bayyana.

Ogunlesi, wanda shine hadimin Buhari kan kafafen yada labaran zamani, ya ce gwamnati ta yanke shawaran haka ne ranar Laraba a taron majalisar zartarwa a Abuja.

A jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook, ya ruwaito Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da cewa an yanke shawaran dawo da tsarin ne bayan shawari da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen gwamnati irinsu kungiyoyin sufuri na NURTW da RTEAN, dss.

Da duminsa: Gwamnatin Buhari zata koma amsan kudin 'Toll Gate' hannun masu motoci
Da duminsa: Gwamnatin Buhari zata koma amsan kudin 'Toll Gate' hannun mutane Hoto: Ministry of Works
Asali: UGC

Yace:

"Majalisar zartaswa ta amince da tsarin amsan kudin Tooll Gate a Legas da Abuja, da kuma Lekki da Ikoyi."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri kan tafiya kasar waje

"Manyan tituna mallakin gwamnatin tarayya masu hanyoyi biyu kadai za'a rika amsan kudi. Ba za'a amshi kudi a tituna masu hanyoyi guda ba."
"Za'a yi amfani da kudin ne wajen gyare-gyaren hanyoyin da kuma biyan masu sanya hannun jari da suka sanya kudinsu wajen karasa ginin titunan."
"Za'a fifita biyan kudi ta hanyoyin zamani sabanin hannu da hannu."

Ya lissafa kudin da kowace mota zata biya kamar haka:

Kananan motoci: N200

Manyan Motoci: N300

Manyan motocin haya: N150

Motocin Luxuries da tankoki: N500

Abubuwan hawan da aka togaciye daga wannan tsarin sune:

Kekuna

A daidaita sahu

Babura

Motocin Diflomasiyya

Sojoji

Jami'an tsaro

Asali: Legit.ng

Online view pixel