Idan zaben 2023 ya zo, Bola Tinubu bai da satifiket da zai nuna ya yi karatu inji Bode George

Idan zaben 2023 ya zo, Bola Tinubu bai da satifiket da zai nuna ya yi karatu inji Bode George

  • Bode George ya yi wa Adeseye Ogunlewe raddi a kan tallar Bola Tinubu a 2023
  • Jagoran na PDP ya ce zai tashi daga ‘Dan Najeriya idan Tinubu ya samu mulki
  • George yayi wa masu goyon-bayan Tinubu kudin goro, yace ba a daidai suke ba

Ogunlewe ya san Tinubu bai mallaki satifiket ba

Legas - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Bode George ya fito ya na cewa Bola Tinubu bai da wata takardar shaidar zuwa makaranta.

Jaridar The Cable ta rahoto Bode George yana maida martani ga Adeseye Ogunlewe wanda ke cewa Bola Tinubu ya kamata ya gaji Muhammadu Buhari.

‘Dan adawar ya ce ian aka tsaida Tinubu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, bai da satifiket da zai gabatar da ke nuna ya yi firamare, sakandare da jami’a.

“Ogunlewe ya san ko Naira nawa aka ce za a bada, Tinubu ba zai iya kawo takardun makarantarsa ba (firamare, sakandare, da jami’a), domin ya san bai da su.”

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Da ake hira da tsohon gwamnan a gidan talabijin, ya ce babu wani mai hankali da zai goyi bayan Tinubu, ya zargi tsohon gwamnan da satar kudin jihar Legas.

George yake cewa Tinubu ya na wawurar biliyoyi har yau daga asusun gwamnatin jihar Legas ta karkashin kamfaninsa na Alpha Beta da ke tattara haraji.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Gwamnan Kano Hoto: koko.ng
Asali: UGC

Me George zai yi idan hakan ta faru?

Har ta kai Premium Times ta rahoto George yana cewa zai tashi daga zama ‘dan Najeriya idan jagoran na jam’iyyar APC mai mulki, ya karbi mulkin kasar nan.

“Zan yi duk abin da zan iya in tashi daga zama ‘dan kasa idan hakan ta faru. Mutum irin wannan? Shin ka na tunanin jihar Legas za ta ga wani canji ne?
“A nan (Legas) muke zaune, dubi jihar. Babu hanyoyin ruwa, ka duba abin da suka yi a bakin teku.”

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

“In tsaya ina tunani a rain a cewa irin wannan mutum zai zama shugaban kasa…Ka je ka duba dukkaninsu (masu goyon bayan Tinubu), wani abu yana damunsu.”

Cif George ya zargi Ogunlewe da yin baki-biyu, yace idan aka binciko bayanan da ya yi a da, za a ji yana sukar Tinubu, sai ga shi yana tallarsa bayan ya dawo APC.

APC za ta yi shari'a da 'ya 'yan ta a Ondo

A makon nan aka ji cewa wasu ‘ya 'yan APC sun kai jam’iyyarsu kotu, suna so a ruguza zabukan mazabu da aka yi, a cewarsu rashin adalci ya sa suka garzaya kotun.

Wannan mataki da fusatattun 'yan jam'iyyar suka dauka ya saba umarnin da majalisar NEC ta bada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel