Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri kan tafiya kasar waje

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri kan tafiya kasar waje

  • Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa take da tsauri wajen ka'idojin tafiye-tafiye
  • Gwamnat ta ce wannan ba komai bane face nema wa 'yan kasar sauki wajen kare kansu
  • Gwamnatin ta kuma ce, ta ware wasu kasashe da tace su ne kasashe masu hadarin gaske

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ce ta sanya tsauraran ka'idojin balaguro zuwa kasashen waje ne don kare 'yan kasar daga kamuwa da cutar ta Korona, Punch ta ruwaito.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Laraba 11 ga awatan Agusta.

Mohammed ya ce an sanya Najeriya a matsayin kasa mai tsaurin ra'ayi dangane da ka'idojin tafiye-tafiye, yana mai bayanin cewa matsayin gwamnati shi ne kare mutanenta daga yaduwar cutar.

Dalilin da yasa gwamnatinmu ke da tsauri game da yawan tafiya kasar waje, Lai Mohammed
Lai Mohammed - Hoto: dailytust.com
Asali: UGC

A cewarsa:

"An zarge mu da cewa dokokin mu suna da tsauri. Mun ce a'a. Ba mu kasance masu tauri saboda taurin kai ba. Muna da tauri ne saboda abin da kimiyya ke bukata. Muna da tsauri ne saboda muna son kare mutanen mu.

Kara karanta wannan

Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya

Ministan ya bayyana cewa, Najeriya ta sanya wasu kasashe ne a jerin kasashe masu hadari kasancewar bullar annobar Korona nau'in Delta.

“Mun sanya musu suna kebabbun kasashe da aka sanya wa takunkumi. Ya zuwa yau, muna da guda hudu kadai irin wannan; Afirka ta Kudu, Indiya, Brazil da Turkiya.

"Kuma akwai tsauraran ka'idojin balaguro a kan wadannan kasashe saboda muna son hanawa da kare mutanenmu.

Na kusa da Buhari suna kangeshi da masu fada masa gaskiya, Dalung

Tsohon ministan wasanni da harkokin matasa, barista Solomon Dalung, ya koka kan yadda wasu makusanta shugaban kasa Muhammadu Buhari a mulki suke kange shi da masu kokarin ganin sun daura shi a turba ta gari da yi wa 'yan kasa hidima.

Dalung ya kuma bayyana cewa, na kusa da shugaban sukan ba da uzurin bogi na cewa, akwai annobar Korona don haka ba za a iya gana wa da shugaban ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da wakilinmu a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.

A karon farko, gwamnatin Buhari ta ware wa 'yan sanda kudin sayen man fetur

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta amince da ware naira biliyan hudu na man motocin aiki na 'yan sanda a fadin jihohi 36 na kasar hadi da Abuja, BBC Hausa ta ruwaito.

An ruwaito cewa, ministan ma’aikatar harkokin 'yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da haka a Abuja a ranar Talata.

Ministan ya ce kudin wanda aka ware a kasafin 2021 shi ne karon farko da aka ware wa 'yan sanda kudin fetur kaso mai tsoka a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.