Yarbawa sun gargadi Obasanjo kan shiga fadan Sunday Igboho da gwamnatin Buhari

Yarbawa sun gargadi Obasanjo kan shiga fadan Sunday Igboho da gwamnatin Buhari

  • Kungiyar Yarbawa ta shawarci tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo da ya raba kansa da batun Igboho
  • Wannan ya biyo bayan labarin da ake yadawa cewa, Obasanjo ya je Benin domin kubutar da Sunday Igboho
  • Kungiyar ta bayyana yadda Obasanjo ya mori hadin kan Najeriya, tana mai martani mai zafi kan batun

Wata kungiya mai suna Yoruba for One Nigeria Forum (YONF), ta nemi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya janye kansa daga rahoton da ke cewa yana lallabin Jamhuriyar Benin don kare Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho daga fuskantar hukunci.

Kungiyar a cikin wata sanarwa mai taken, 'Olusegun Obasanjo shine babban mai cin gajiyar Hadin kan Najeriya' wanda Seun Adebayo Lawal, shugabanta na kasa ya sanya wa hannu, ya ce kiran ya zama tilas duba da irin fa'idodin da tsohon shugaban kasa daga hadin kan Najeriya.

Yarbawa sun gargadi Obasanjo kan shiga fadan Sunda Igboho da gwamnatin Buhari
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Obasanjo | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito daga wata sanarwar da kungiyar ke martani ga jita-jitar da ake yada wa kan cewa Obasanjo na tsoma baki wajen kubutar Igboho, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

"Tarihin Najeriya, a halin yanzu ya tabbatar da al'ummar Yarbawa a matsayin manyan masu cin gajiyar hadin kan Najeriya tun samun 'yancin kai.
"Abin mamaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo dan kabilar Yarbawa ne wanda ya fi kowa cin gajiyar duk wani abin da Najeriya ta samu na hadin kan ta.
"Obasanjo shi ne dan Najeriya daya tilo daga zuriyar Yarbawa wanda ya taba mulkin kasar nan a karkashin mulkin soja da farar hula.
"Me kuma Najeriya za ta iya yi masa ko al'ummar Yarbawa? Wadanne bukatu ne suka cancanci al’ummar Yarbawa da Obasanjo bai iya yi ba a lokacin da yake Shugaban mulkin soja da Shugaban kasa?
"Ba ya bukatar a tunatar da shi irin rawar da hadin kan Najeriya ta taka a lokacinsa, a matsayinsa na Soja da Shugaban farar hula, don haka, abin da ya kamata ya yiwa al’umma shi ne yin kira ga zaman lafiya, ingantawa da bayar da shawarwari ga Najeriya don hada kai guda daya.

Kara karanta wannan

Kungiyar Yarbawa ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya shiga batun kame Igboho

Kungiyar Yarbawa ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya shiga batun kame Igboho

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere, ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya gana da shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon, don shiga tsakani a lamarin Sunday Igboho.

An tabbatar da ganawar tasu a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, ta hannun mataimaki na musamman kan yada labarai ga Obasanjo, Kehinde Akinyemi, PM News ta ruwaito.

Akinyemi ya ce:

"Obasanjo yana Jamhuriyar Benin a ranar Litinin kuma ya gana da Shugaban kasa amma babu wanda ya san abin da suka tattauna."

Sai dai, Afenifere, a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, ta ce Obasanjo ya kutsa cikin lamarin Igboho ne saboda baya son a dawo dashi Najeriya daga jamhuriyar Benin.

Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

A wani labarin, Yayin da ake tattaunawa game da wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023, masana sun bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar da yafi nagarta, kamar yadda yazo a kuri'ar da jaridar ThisDay ta yi.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho mafaka da afuwa

Kuri'ar ya biyo bayan hirar da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida yayi da gidan talabijin na Arise TV akan wanda zai zama shugaban Najeriya a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel