Kungiyar Yarbawa ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya shiga batun kame Igboho

Kungiyar Yarbawa ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya shiga batun kame Igboho

  • Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya sa baki a lamarin Sunday Igboho
  • A cewar kungiyar, Obasanjo bai yi imanin cewa Igboho zai samu adalci daga gwamnatin Najeriya ba
  • Wannan na zuwa ne bayan da Obasanjo ya gana da shugaban Benin kan batun na Sunday Igboho

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere, ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya gana da shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon, don shiga tsakani a lamarin Sunday Igboho.

An tabbatar da ganawar tasu a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, ta hannun mataimaki na musamman kan yada labarai ga Obasanjo, Kehinde Akinyemi, PM News ta ruwaito.

Kungiyar Yarbawa ta bayyana dalilin da yasa Obasanjo ya shiga batun kame Igboho
Olusegun Obasanjo | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: UGC

Akinyemi ya ce:

"Obasanjo yana Jamhuriyar Benin a ranar Litinin kuma ya gana da Shugaban kasa amma babu wanda ya san abin da suka tattauna."

Sai dai, Afenifere, a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, ta ce Obasanjo ya kutsa cikin lamarin Igboho ne saboda baya son a dawo dashi Najeriya daga jamhuriyar Benin.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho mafaka da afuwa

Igboho ba zai samu adalci a Najeriya ba

A cewar Afenifere, Obasanjo bai yi imanin cewa Igboho zai samu adalci ba idan aka mika shi ga gwamnatin Najeriya daga Jamhuriyar Benin.

Sakataren shirye-shirye na Afenifere, Apogun Kola Omololu, ya ce:

“Obasanjo dan Yarbawa ne da farko dai kafin zama shugaban kasa. Shugabannin Yarbawa ba masu surutu bane, basa yin hayaniya, suna yin aiki. Dubi yadda muka yi yakin NADECO, an yi shi cike da hankali.

A cewar kungiyar, sarakunan Yarbawa da sauran manyan mutane ba za su bari a mika Igboho ga gwamnatin Najeriya ba, inji rahoton The Punch.

Jerin sabbin manyan laifuka 3 da jamhuriyar Benin ke tuhumar Sunday Igboho akai

A wani labarin, Ibrahim Salami, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Igboho ya bayyana cewa an bijiro da sabbin tuhume-tuhume a kan Sunday Igboho a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, yayin zaman kotu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Wadannan su ne uku daga cikin manyan laifukan da gwamnatin jamhuriyar Benin ke tuhumar Igboho akai:

1. Hijira ba bisa ka'ida ba

2. Hadin baki da jami'an shige da fice

3. Kokarin haifar da tarzoma

Asali: Legit.ng

Online view pixel