Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne

Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne

  • Aminu Yar'adua 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne
  • An gano Aminu ma'aikaci ne ga Alhaji Atiku Abubakar
  • Masu hakkin jini sun ce a biya su diyyar N15m

Katsina - Sabbin bayanai sun bayyana game da dan gidan Yar'adua da aka garkame a kurkuku kan zargin kisan mutum hudu sakamakon hadarin mota a Yola, birnin jihar Adamawa ranar Alhamis.

Sabanin labaran da aka ruwaito cewa 'dan gidan tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ne, an gano cewa ba haka bane, 'dan marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua ne, rahoton ThisDay.

Wata majiya daga gidan Yar'adua, wanda ya bukacia a sakaye sunansa, ya ce Aminu, ma'aikaci ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ne.

Majiyar ta kara da cewa an yi wannan fayyacewar ne ba don nisantashi da iyalin Yar'adua ba, amma don kawai bayyanawa jama'a gaskiyar lamari.

Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane
Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Alkali ta tsare Aminu ‘Yar’adua a gidan yari bisa zargin kashe mutum 4

Kara karanta wannan

Alkali ta tsare ‘Dan cikin Marigayi Ummaru ‘Yar’adua a gidan yari bisa zargin kashe mutum 4

A ranar Alhamis, kotun majistare da ke zama a garin Yola, jihar Adamawa, ta tsare ‘dan tsohon shugaban Najeriya, Aminu Yar’Adua, a gidan yari.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta ce Alkali ya bukaci a rike Aminu Yar’Adua mai shekara 36 ne saboda zarginsa da laifin kashe wasu mutane hudu a Yola.

A cewar NAN, dalibin na jami’ar Amurka da ke Najeriya watau AUN, ya jawo wani mummunan hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Bayin Allah kwanaki.

Ana zargin cewa gangancinsa ne ya kai ga faruwar wannan hadari a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, 2021.

Masu hakkin jini sun ce a biya su diyyar N15m

“Wanda suka mutu a hadarin su ne; Aisha Umar (30), Aisha Mamadu (32), Suleiman Abubakar (2) and Jummai Abubakar (30)."
"Sai kuma Rejoice Annu (28) and Hajara Aliyu (27) da sun samu rauni.”

Jami’in da ya ke karar ‘Yar’adua ya shaida wa kotu cewa ‘yan uwan Aisha Umar, Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar suna neman N15m a matsayin diyya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin mulkin Abacha ya kwanta dama

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng