Sarkin Musulmi ya koka kan halin yunwar da al’umma ke ciki, ya ce abubuwa na kara birkicewa
- Sultan Sa’ad Abubakar III ya yi jawabi a taron zaman lafiya da aka shirya a Gombe
- Mai alfarma Sarkin Musulmin ya ce farashin kayan abinci suna ta tashi a Najeriya
- Sultan yace idan jama’a suna zama da yunwa, ba za a taba samun zaman lafiya ba
Gombe - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Mohammed Sa'ad Abubakar III, ya ce abubuwa suna kara tabarbare wa a Najeriya, ana fama da karancin abinci.
Yunwa ba ta da hankali
Sultan Mohammed Saad Abubakar III ya bayyana cewa rashin isasshen abinci ya na jawo rashin tsaro.
Punch ta rahoto Sarkin Musulmi ya na cewa yunwa ba ta da hankali yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, 2021 a Gombe.
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana ne a kan hadin-kai a Najeriya a wajen wani taro da majalisar Da’wah Coordination Council of Nigeria ta shirya.
Sultan yake cewa matsalolin ‘yan Najeriya kullum dada karu wa yake yi a halin da ake ciki, Mohammed Saad Abubakar yace abubuwa ba kyau suke yi ba.
Babu addinin da ya ce a kashe rai - Sultan
“Abin da mu ka rasa a kasar nan shi ne gaskiya da fada wa kanmu gaskiya wajen yin abin da zai fishe mu, domin babu addinin da ya ce a kashe mutum.”
“Ta’addanci, tada zaune-tsaye da garkuwa da mutane su na ci, kuma masu wannan aiki suna yawo abinsu.”
“Mutane da yawa suna cikin yunwa, domin ba za su iya sayen abinci ba; farashi ya na kara tashi sama kullum. A tabbatar akwai abinci saboda talaka ya samu.”
“Idan babu abinci, babu zaman lafiya, idan babu zaman lafiya, babu tsaro, idan babu tsaro, babu cigaba, idan babu cigaba, za mu rika rayuwa ne haka kurum.”
Jaridar ta ce limamin kiristan nan, John Onaiyekan ya yi jawabi a taron ta bakin Rabaren Father Joseph Shinga, inda ya yi kira ga al’umma su zauna lafiya da junansu.
Sauran wadanda suka tofa albarkacin bakinsu, sun hada da Sarkin Gombe, Mai martaba, Abubakar Shehu Abubakar III da gwamna, Muhammad Inuwa Yahaya.
Babu zaman lafiya a jihar Shugaban kasa
Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi halin rashin tsaro da suke ciki, ya ce kullum sai ‘Yan bindiga sun yi wa mata fyade a kananan hukumomi 10 a jihar Katsina
Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya ce duk ranar Allah, miyagun ‘yaan bindiga su kan yi ta’adi a jiharsa
Asali: Legit.ng