Rikicin PDP ya yi muni yayin da aka nemi shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ya yi murabus
- Kungiyar PDP ta Arewa ta ce tana adawa da ci gaba da kasancewar Uche Secondus a matsayin shugaban jam'iyyar adawa na kasa
- Kungiyar ta arewa ta bayyana dalilin da ya sa ya kamata a gaggauta maye gurbin shugaban na kasa da wani jami'i
- Ta bayyana matakan da za ta dauka don nuna rashin amincewa da shugabancin shugaban jam’iyyar na kasa
Ga dukkan alamu, rikicin da ke girgiza Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ci gaba da ƙaruwa duba da buƙatar da ƙungiyar PDP a Arewa ta gabatar na murabus ɗin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Uche Secondus.
Kungiyar ta arewa wadda ta yi ikirarin wakiltar muradun 'yan siyasa daga jihohin arewa 19 da Abuja, ta bukaci Secondus da ya sauka daga kujerarsa domin ceto jam'iyyar daga durkushewa baki daya.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa kungiyar ta gabatar da wannan bukatar ne a wani taron manema labarai a jihar Kaduna a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta.
2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa a Arewa, Yahaya Salisu, ya yi zargin cewa gazawar Secondus ne ya sanya jam’iyyar PDP ta rasa mambobi masu kishi zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC).
Yace:
"Muna son yin kira ga Shugaban Jam'iyyar na kasa, Uche Secondus da yayi murabus cikin gaggawa, don kare jam'iyyarmu daga durkushewa, kamar yadda muka rigada, muka rasa Gwamnoni, memba na BoT, Jami'an kasa, Sanatoci, membobin majalisar wakilai da yawa zuwa APC. ''
Kungiyar ta yi barazanar tattara mambobinta don yin taro a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja idan shugabancin jam'iyyar ya gaza neman shugaban jam'iyyar na kasa ya yi murabus.
Jagoran kungiyar na Arewa PDP ya yi bayanin cewa mambobin kungiyar suma za su fice daga jam’iyyar da gaggawa idan Secondus ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar na kasa.
Rigimar cikin gidan PDP ta kara cabewa, wasu jerin shugabanni na barazanar murabus kwanan nan
A gefe guda, mun ji cewa wasu mutum hudu daga cikin ‘yan majalisar aiwatar wa watau NWC na jam’iyyar adawa ta PDP, suna barazanar sauka daga kujerunsu.
Rahoton ya bayyana cewa wadannan shugabanni hudu suna barazanar yin murabus idan jam’iyyar ta gagara kawo karshen rikicin da ake ta fama da shi.
Asali: Legit.ng