Tirkashi: Bidiyon jerin motocin alfarma na Floyd Mayweather ya gigita jama'a

Tirkashi: Bidiyon jerin motocin alfarma na Floyd Mayweather ya gigita jama'a

  • Babu shakka tsohon dan dambe Floyd Mayweather yana da tarin dukiya wacce yake alfahari da mallakarta
  • A wani bidyo da ya fitar a shafinsa na Instagram, an ga jerin kasaitattun motocin alfarma dake jere reras a garejinsa
  • Daga ciki akwai Bugatti Veyronsu guda uku, Ferrari 458 Spiders guda biyu tare da Lamborghini Aventador, Rolls Royce

Las Vegas - Babu shakka tsohon dan dambe Floyd Mayweather yana da tarin dukiya kuma yana son hawa motocin alfarma na zamani.

Fitaccen dan damben mai suna Floyd Mayweather wanda aka fi sani da Money, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram.

Sanannen abu ne cewa ma'abota son kyale-kyale da kayan kawa cikin samari da 'yan mata ne suka cika shafin mai tarin arzikin.

Tirkashi: Bidiyon jerin motocin alfarma na Floyd Mayweather ya gigita jama'a
Tirkashi: Bidiyon jerin motocin alfarma na Floyd Mayweather ya gigita jama'a. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Da safiyar Asabar ne ya wallafa bidiyon wanda ke nuna jerin motocinsa na alfarma wadanda yake hawa.

Ko shakka babu idan aka kalla jerin motocin an san kudi mai tarin yawa ne suka siyesu ba na wasa ba.

Kirar motocin dake garejin

Tsohon dan damben yana da arzikin da ya kai $450. Ya mallaki motoci kirar Bugatti Veyronsu guda uku, Ferrari 458 Spiders guda biyu tare da Lamborghini Aventador, Rolls Royce, Porsche 911 Turbo S da Ferrari 599 GTB Fiorano.

Wadannan jerin motocin na alfarma suna nan ne jere a wani gareji da yayi a gidansa na kasan kasa wanda ya kashewa miliyan £20.

Ga bidiyon kamar yadda ya wallafa a Instagram domin mai karatu ya kashe kwarkwatar ido:

Sifetan dan sanda da 'yan bindiga 3 sun sheke a farmakin da miyagu suka kai caji ofis

Miyagun 'yan bindiga a ranar Alhamis sun kone ofishin 'yan sanda na Orlu inda suka halaka dan sanda mai mukamin sifeta.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an halaka uku daga cikin 'yan bindigan bayan musayar wuta da aka yi tsakanin miyagun da 'yan sandan.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan, CSP Mike Abattam, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a. Lamarin ya faru wurin karfe 9 da rabi na dare yayin da 'yan bindigan masu yawa dauke da makamai suka kai farmaki kuma suka dinga jefa bama-bamai kan rufin ofishin 'yan sanda na Orlu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel