Sifetan dan sanda da 'yan bindiga 3 sun sheke a farmakin da miyagu suka kai caji ofis

Sifetan dan sanda da 'yan bindiga 3 sun sheke a farmakin da miyagu suka kai caji ofis

  • 'Yan bindiga sun bankawa ofishin 'yan sanda dake Orlu a jihar Imo wuta inda ya kone kurmus
  • An gano cewa miyagun sun dinga wurga bama-bamai ofishin inda 'yan sanda suka sakar musu ruwan wuta
  • 'Yan sandan sun yi nasarar sheke 'yan bindiga 3 yayin da sifetan dan sanda daya ya halaka yayin artabun

Orlu, Imo - Miyagun 'yan bindiga a ranar Alhamis sun kone ofishin 'yan sanda na Orlu inda suka halaka dan sanda mai mukamin sifeta.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an halaka uku daga cikin 'yan bindigan bayan musayar wuta da aka yi tsakanin miyagun da 'yan sandan.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan, CSP Mike Abattam, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a.

Lamarin ya faru wurin karfe 9 da rabi na dare yayin da 'yan bindigan masu yawa dauke da makamai suka kai farmaki kuma suka dinga jefa bama-bamai kan rufin ofishin 'yan sanda na Orlu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mutum 1 ya sheka lahira yayin da 'yan fashi suka kai farmaki bankuna 2

Sifetan dan sanda da 'yan bindiga 3 sun sheke a farmakin da miyagu suka kai caji ofis
Sifetan dan sanda da 'yan bindiga 3 sun sheke a farmakin da miyagu suka kai caji ofis. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sifetan dan sanda ya rasa ransa

Yace muguwar wutar da ta tashi a ofishin 'yan sandan ta shafi wasu ababen hawa dake farfajiyar caji ofis din.

Amma kuma Abattam ya ce 'yan sandan sun yi martani ga 'yan bindigan kuma ruwan wuta yasa 'yan bindigan suka yi laushi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takardar ta ce:

Uku daga cikin 'yan bindigan sun sheka lahira kuma an samu bindigoginsu yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji da raunika. Amma cike da jimami an rasa ran sifetan dan sanda yayin farmakin.

Matasan PDP sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP

Matasan jam’iyyar PDP sun yi wa tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, wankin babban bargo akan alakanta jam’iyyarsu da APC, Daily Trust ta wallafa.

Shugabannin jam’iyyar adawar ta PDP sun koka da Jega akan rashin nunawa ‘yan Najeriya gaskiya saboda suna zarginsa da zama daya daga cikin wadanda suka dakatar da cigaban Najeriya tun 2015.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa, Sun Kame Wasu a Benuwai

A wata takarda wacce shugaban jam’iyyar na kasa, Salaudeen A. Lukman ya sanya hannu, matasan PDP sun nuna takaicin su akan maganganun da tsohon shugaban INEC din yayi a BBC akan zargin ko dai da gangan yake yi don ya rudar da jama’a ko kuma salo ne na tallata sabuwar jam’iyyarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel