Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

  • Cece-kuce sun barke bayan tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida yace mulkinsa ya yi yaki da rashawa fiye da mulkin Muhammadu Buhari
  • IBB ya tunatar da lokacin da ya sauke gwamna kan ya saci N313,000 amma kuma a yau masu mulki suna satar biliyoyi kuma suna tafe hankali kwance
  • Wadannan maganganun nashi sun janyo surutai iri-iri har wasu suke bin bayansa yayin da wasu kuma suka ki amincewa da wannan batun nashi

Minna, Niger - Cece-kuce ya barke tun bayan wani tattaunawa da aka yi da tsohon shugaban kasa na mulkin soji a ARISE TV inda yace mulkinsa ya yi yaki da cin hanci da rashawa fiye da mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

IBB ya tunatar da yadda ya sauke gwamna akan satar N313,000 amma a halin yanzu mutane da dama da suka saci biliyoyin nairori suna yawonsu a cikin kasar nan.

Kara karanta wannan

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari
Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan furucin nashi ya janyo cece-kuce, wasu suna sukar maganarsa yayin da wasu suka amince da maganarsa inda suke cewa rashawa tana kara yawaita a Najeriya.

Ga wasu daga cikin martanin jama'a

Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama'a. Misali daya daga cikin masu tsokaci ya zargi IBB da zama tushen rashawa a Najeriya.

A tarihi, IBB shine ya halasta rashawa a Najeriya,” a cewar wani Tunde Ayankoya a Twitter.

Wani Chris Ngonadi yace:

Tunda ba a rufeshi ba, mai zai hana yayi ta surutai. Ba laifin shi bane wannan shirmen da yake yi.

Amma duk da haka, akwai wadanda suke goyon bayan IBB inda suke cewa ta yuwu gaskiya ne.

A cewarsu baya ga rashawa, mulkin Buhari ta janyo ta’addanci mai yawan gaske.

Wani wanda yayi martani mai suna Danielmechi yace:

Babu ta’addanci a lokacin IBB, a lokacin mutanen kirki aka daura don su tafiyar da al’amuran kasa. Kuma cin hanci da rashawa bai yawaita ba.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba

Tsohon shugaban kasan mulki soja, Ibrahim Babangida ya kara yin magana kan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 inda yace babu shakka mummunan juyin mulki za a tafka a kasar nan da ba a soke shi ba.

Zaben an yi shi ne tsakanin Bashir Tofa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) da MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Duk da Abiola ne ya ci zaben kamar yadda sakamako ya nuna, an soke zaben tun kafin jami'ai su bada sanarwan wanda yayi nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel