Tsohon sanatan Najeriya ya mayar da martani bayan hotonsa ya sake bayyana tare da dan damfara, Hushpuppi

Tsohon sanatan Najeriya ya mayar da martani bayan hotonsa ya sake bayyana tare da dan damfara, Hushpuppi

  • Tsohon dan majalisar dattijan Najeriya, Dino Melaye, ya yi watsi da hasashen cewa yana jin kunyan hoton da ya dauka tare da dan damfara da aka kama, Hushpuppi
  • Dan siyasar a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa ba shi da dalilin boyewa saboda hoton da ya dauka tare da wani
  • Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi, a yanzu haka yana fuskantar shari'a a wata kotun Amurka bisa zargin zamba

Ga dukkan alamu, tsohon sanatan Najeriya, Dino Melaye, bai damu da yada hotonsa da ake yi ba tare da ɗan damfara, Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Melaye a cikin wata sanarwa ta shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi kira ga jama’a da su daina yada hotunansa da fitaccen dan damfara.

Tsohon sanatan Najeriya ya mayar da martani bayan hotonsa ya sake bayyana tare da dan damfara, Hushpuppi
Dino Melaye ya ce babu wani dalili da zai sa ya hana mutane yada hotonsa tare da Hushpuppi Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

Ya bukaci duk wanda ke son yada hotonsa da Hushpuppi da ya yi hakan.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Ya ce:

“Babu wani lokaci da na nemi mutane da su daina sanya hotunana tare da Hushpuppi ko wani don wannan lamarin saboda babu dalilin hakan.
“Ni mashahurin dan siyasa ne, don Allah a ci gaba da yadawa jare. Abun da tsuntsu ya ci da shi zai tashi. SDM ''

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

A wani labarin, Ofishin ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Kara karanta wannan

Ya dasa sabon zargi: Abba Kyari ya goge wallafar da yayi a shafinsa inda yayi bayanin alakarsa da Huspuppi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng