Da duminsa: An ceto karin mutum daya cikin yan makarantan Chibok, Zulum

Da duminsa: An ceto karin mutum daya cikin yan makarantan Chibok, Zulum

  • Bayan shekara 7, an gano daya daga cikin yan matan Chibok
  • An aurar da ita ga daya daga cikin yan ta'addan Boko Haram
  • Sama da yan Boko Haram 100 sun mika wuya a makon nan kadai

An ceto karin mutum daya cikin yan matan Chibok da aka sace a 2014, gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan ranar Asabar.

Yarinyar da aka ceto ta auri wani dan ta'addan Boko Haram ne kuma ta haifa masa yara biyu, gwamnan ya bayyana a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri.

A ranar 14 ga Afrilu, 2014, yan ta'addan Boko Haram sun yi awon gaba da dalibai mata kimanin 276 daga makarantar sakandaren mata dake Chibok, jihar Borno.

Karin yan Boko Haram 19 sun mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno

An samu sabon nasara a yaki da yan ta'adda yayinda wasu yan Boko Haram/ISWAP suka mika wuya ga rundunar FOB dake Bama, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Sojoji 24 a kasar Chadi

A jawabin da Diraktan yada labarai na hukumar Soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya saki ranar Laraba, 4 ga Agusta, yace mayaka 14 tare da iyalansu suka mika wuya.

Nwachukwu ya ce Sojojin sun karbi tubabbun yan ta'addan ne a cikin dajin Sambisa ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.

Da duminsa: An ceto karin mutum daya cikin yan makarantan Chibok, Gwamna Zulum
Da duminsa: An ceto karin mutum daya cikin yan makarantan Chibok, Zulum Hoto: Presidency

Bayan shekaru 7, ban fidda rai za'a ceto 'yan matan Chibok ba: Gwamna Babagana Zulum

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ce da sannu za'a ceto dalibai matan da yan ta'addan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren Chibok a 2014.

Zulum ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki bayan shekaru bakwai da yan Boko Haram sukayi awon gaba da daliban yayinda suke shirin rubuta jarabawa.

Duk da cewa an ceto wasu daga cikin yaran, har yanzu akwai sauran daliban na hannun yan ta'addan.

A cewar Zulum, a matsayinsa na uba, ba zai iya jure ciwon rasa diya mace tsawon shekaru bakwai hannun yan ta'adda ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng