An Cafke Bata Garin da Suka Lakada wa Jami'an Kashe Gobara Duka a Abuja

An Cafke Bata Garin da Suka Lakada wa Jami'an Kashe Gobara Duka a Abuja

  • Wasu ’yan daba sun kai wa ma’aikatan kashe gobara hari a yankin Gwarimpa da ke Abuja yayin da suke aikin ceto a ranar Juma’a
  • Rahoto ya nuna cewa harin ya jikkata daya daga cikin ma’aikatan, wanda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci
  • Hukumar kashe gobara ta ce an kama wadanda ake zargi da kai harin, kuma yanzu haka suna fuskantar bincike a wajen hukuma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS), reshen babban birnin tarayya Abuja, ta yi Allah wadai da harin da wasu mutane suka kai wa ma’aikatanta a yankin Gwarimpa yayin da suke aikin kashe gobara.

Kakakin hukumar a Abuja, Barnabas Anyam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce harin ya jikkata daya daga cikin ma’aikatan da ke aikin ceto.

Kara karanta wannan

Abin da ake zargi ya tabbata, jagoran ƴan bindiga ya faɗi dalilansu na ɗaukar makami

Jami'an kashe gobara
Masu kashe gobara suna bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Yadda aka kai wa ma’aikatan hari

Punch ta wallafa cewa Anyam ya ce ma’aikatan kashe gobarar daga ofishin hukumar da ke Kubwa sun samu kiran gaggawa daga wata mata mazauniyar yankin a safiyar ranar Juma’a.

A yayin da suka isa wurin domin gudanar da aikin ceto, wasu da ake zargin ’yan daba ne suka far musu da duwatsu.

Kakakin hukumar ya ce daya daga cikin ma’aikatan ya samu rauni a kansa, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

An kai rahoto ofishin ’yan sanda

Bayan faruwar lamarin, hukumar ta bayyana cewa an kai rahoton harin ofishin ’yan sanda da ke unguwar Galadima.

Anyam ya ce wadanda ake zargi da aikata laifin sun shiga hannun jami’an tsaro, kuma ana gudanar da bincike a kansu.

Ya nakalto shugaban hukumar kashe gobara a Abuja, Muhammad Anas, yana bayyana bacin ransa kan yadda ake ci gaba da kai wa ma’aikatan kashe gobara hari yayin da suke gudanar da ayyukansu na hukuma.

Kara karanta wannan

An yi harbe harbe a kusa da White House da Donald Trump yake zama

Hukumar ta gargadi masu ka hari

Anas ya jaddada cewa ya kamata a bar ma’aikatan kashe gobara su gudanar da aikinsu ba tare da fuskantar barazana, cin zarafi ko hari ba.

Ya yi gargadin cewa duk wanda ya kai wa jami’an kashe gobara hari ko ya hana su gudanar da aikin ceto a wurin da gobara ta tashi, zai fuskanci hukunci bisa doka.

Kwanturolan ya kuma bukaci mazauna Abuja su rika taimakawa tare da yaba wa kokarin ma’aikatan kashe gobara, musamman a lokutan da ake gudanar da ayyukan gaggawa.

Taswirar FCT Abuja
Taswirar FCT Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya shawarci jama’a da su guji duk wani hali na kai wa jami’an hari, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da kokarin samar da agajin gaggawa cikin sauri da inganci a babban birnin tarayya.

Gargadin Tinubu kan kai hari

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da karuwar tashe-tashen hankula a harkokin siyasa a sassan Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

Tinubu ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani hali na rashin da’a da zai iya haddasa rikici ko kawo cikas ga zaman lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar ya bayyana cewa ba za a lamunci duk wani rashin da’a daga ’yan siyasa da magoya bayansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng